Biliyan Ɗari shida da Miliyan ɗari biyu da Hamsin, Tallafi daga Gwamnatin Tarayya domin ɓunƙasa Karkara da gandun Daji a jihar Katsina…..

A ranar Alhamis ne, 21 ga watan Janairu Wakilan Katsina City News sun samu Zantawa da mai bawa Gwamnan Katsina Shawara, akan Dabbobi da gandun Daji, Dakta Lawal Usman Bagiwa, kan wasu kuɗaɗe da Gwamnatin tarayya ta aike dasu ga Gwamnatin jihar Katsina domin, raya Karkara da yankunan Fulani makiyaya, inda Bagiwa yayi ma Jaridun mu bayani Filla-filla akan irin tsari da akai don samar da ci gaba a yankunan.

Dakta Bagiwa ya faɗaɗa bayanin nasa akan wuraren kiwo, wanda yana ɗaya daga cikin matsalolin da suke ƙara janyo rashin zaman lafiya a yankunan karkara, “Munada wajen kiwo Grazing Reserve) na Ruma Kukar Jangarai wanda faɗinsa yakai Hekta dubu ɗari da Ishirin da ‘yan kai, kuma wannan wajen kiwo ya shafi ƙananan Hukumomi goma, da suka haɗa da Jibiya, Kurfi, Safana, Ƙanƙara, Batsari, Dutsin-ma, Ɗanmusa, Faskari,  Sabuwa da Ɗandume.” Yace “kuma Babbar Matsalar da ake ta fama da ita ta rikicin tsaro, duk kusan a nan suke.” Bagiwa yace sun shirya tsari mai kyau da zai samar da ingantattun ababen more rayuwa, kamar makarantu, Asibitoci, na Dabbobi da na Mutane, samar da Ingantaccen wajen kiwo, haɗa hannu da ‘yan Kasuwa, da samar da tsaftatacciyar Madarar shanu, yace kuma abin farin ciki ba Gwamnati bace tace zatayi waɗannan abubuwan na more rayuwa su mutanen yankin ne da kansu suka ce, ga abinda suke so a wajen. Sakamakon zaman da sukai na tattaunawa da bangarorin Filani, da Wakilan Kungiyoyin su, irin su Kotal Hore, wakilan yan banga da jami’an tsaro, akan yanda za a billoma shirin.

Amma yace, su kudi idan suka zo daga Gwambati ba wai kawai za’a fara kashesu bane kai tsaye ba sai an turawa Majalisa, an maida su Doka, sana. Kuma an kaima majalisa ta maida su Doka Majalisa tasa hannu, Gwamna ya sa hannu. Yanzu an sanya ma su tuntuɓa (Consultants) su tsara, duka Ayyukan, da ma tasawirar Dajin, da kuma yanda za’a kashe kuɗin. Sana kuma su mutanen yankin sunyi Al’ƙawari indai akai masu abinda suke so, zasu kula da samar da tsaro domin ganin anyi aikin cikin nasara.

“Bana fatan wani abu ya faru a lokacin da ake gudanar da Aikin, domin su masu kawo cikas a tsaron su sukace ga abinda suke so, kuma suka ce zasu tsare, don da Muka je don jin ra’ayiyin jama’a a yankin su kansu, sunzo wajen (kodaya yake sunzo a ɓoye saboda akwai tsaro) amma dama ba zasu bayyana cewa suna wajen ba. Kuma mun shiga mun fito lafiya,” Inji Dakta Lawal Bagiwa.

Munada Cikakkiyar firar a Shafin mu na YOUTUBE: Katsina City News TV 📺 dakuma Shafin mu na Facebook,

Zakuma ku iya sauke Application din mu a wayoyin ku na salula idan kukaje Playstor kuka rubuta Katsina City News, zai bayyana sai ku sauke. Akwai shirye-shirye masu faɗakarwa, Ilimantarwa gami da Nishaɗantarwa.

Don ƙarin bayani Tel: ☎️07043777779, 08137777445,

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here