BIKIN YAYE DALIBAI DAGA JAMI’AR ALQALAM UNIVERSITY KATSINA

Daga Wakilinmu

Ana cigaba da bikin yaye Dalibai a Jami’ar Alqalam University daga cikin Birnin Katsina, taron wanda aka fara gudanar da shi da misalin 11:00 na safe ya samu halartar Malamai da Dalibai daga koina a fadin Jahar Katsina.

Bayan gudanar da addu’ah an yii kira da nasiha ga Dalibai da su zama jakadun na kwarai sannan kar su ce dole sai aikin Gwamnati zasu yi, saboda yanayin da ake ciki Gwamnati ba zata iya ba kowa aiki ba, ya kamata kowanenku kar ya raina sana’ah kowace iri ce, Misali kamar Tuka Kurkura, sayar da indomie, Aski ko walda.

Shi kuma wani daga cikin malamai shawara ya baiwa Dalibai musamman mata da kar su ce sai mai Digree zasu aura ko sai kudi, yana da kyau su zaka jakadu na kirki ga Addinin Musulunci da Al’adun Hausawa.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here