Home Photo News BIKIN KONA GAWA A BIRNIN DELHI NA KASAR INDIYA

BIKIN KONA GAWA A BIRNIN DELHI NA KASAR INDIYA

CIKIN HOTUNA: A birnin Delhi na kasar India, ana ta kona gawarwakin wadanda cutar COVID-19 ta kashe, abin da ya kai ga har hukumomin sun fara samun bukatun neman iznin a sare bishiyoyin wuraren shakatawa da ke birnin don kona gawarwakin, yayin da cutar take kokarin fin karfin fannin kiwon lafiyar kasar.

Makabartun da ke wajen birane irinsu Delhi, wanda shi ya fi yawan masu kamuwa da cutar a kowacce rana, motocin daukan marasa lafiya da dama kan yi layi dauke da gawarwakin da za a kona. Kona gawarwakin da ake yi saboda karancin filaye, ya sa da zarar dare ya yi za a ga hasken wutar da ake kona mamatan ya lullube sama.

Voa/-AP

NO COMMENTS

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

%d bloggers like this: