Biden zai haramtawa ƴan Afirka ta Kudu shiga Amurka- bbc

Ana saran shugaban Amurka Joe Biden ya dawo da haramcin shiga ƙasar da Donald Trump ya ɗage kwanaki kafin barin mulki.

A yau Litinin ake saran sake mai do haramcin kan Afirka ta Kudu da Brazil, da ke fama da sabon nau’in annobar korona.

Sannan haramci zai kuma shafi masu shiga ƙasar daga Burtaniya, Ireland da sauran ƙasashen Turai 26.

Matakin gwamnatin tsohon shugaba Trump na ɗage haramcin da ya sanya tun a watan Maris ya fuskanci suka daga sakatariyar yaɗa labaran shugaba Biden, Jen Psaki

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here