Advert
Home Sashen Hausa Bello Turji na neman Yafiya da Zaman Sasanci.....

Bello Turji na neman Yafiya da Zaman Sasanci…..

Muhammadu Aminu Kabir

A wata wasiƙar da mukayi cin karo da ita Mai ɗauke da shafuka Ukku an hakaito cewa Bello Turji wanda aka sani da Kachalla Fakai a Daji ya rubuta saƙo zuwa ga Masarautar Shinkafi, Gwamnan Jihar Zamfara, Shugaban ƙasa Buhari dama Manyan Malamai.

Turji ya nemi a yi zaman sulhu da sassanci a koma kamar yadda ake a baya, a cikin Takardar ya bayyana cewa shi ba Barawo bane Dan haka yana neman a zauna ayi zaman ban hakuri, abar Fulani su riƙa shiga cikin Al-umma suna gudanar da Alamurran su kamar a baya.

Yace ana tsangwama wa Fulani ne da yawa haka yasa suka ɗauki makamai, ya bayyana cewa Idan dai za’a yi zaman bisa Adalci babu Yaudara to a shirye yake ya anso duk wani Makami da ake amfani dashi cikin Daji.

Kazalika ya Buƙaci cewa Idan za’a yi zaman ya kasance akwai Malamai a ciki kuma Sheikh Ahamed Mahmud Gumi ya kasance cikin Malaman da za’a yi zaman dasu, ya bayyana cewa dalilin sako shi ciki shine a baya yaje wurin su yayi masu Wa’azi kuma sunga amfanin Wa’azin.

Shin Ko yaushe wannan Takardar ta fita ? shine abinda bamu da tabbas kuma kawo yanzu dai bamu San sahihancin ita wannan Takardar ba.

A dai cikin Satin nan ne Jami’an tsaron Najeriya sukayi dirar mikiya a Dajin Isa da sabon Birni na jihar Sokoto Inda sukayi Luguden ruwan wuta a Dajin Wanda aka bayyana cewa yayi sanadiyyar Mutuwar Ƴan Ta’adar Dajin da dama.

KATSINA CITY NEWShttps://www.katsinacitynews.com
Danjuma Katsina, Dan Jarida, Manazarci, Marubuci, Mamallakin Jaridun KATSINA CITY NEWS, JARIDAR TASKAR LABARAI, THE LINKS NEWS, a karkashin Kamfanin MATASA MEDIA LINKS NIGERIAN LTD

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Must Read

Jam’iyyar PDP a Katsina ta sanar da kuɗin form ɗin takarar shugabannin ƙananan hukumomi da kansiloli a zaɓe mai zuwa

Jam'iyyar PDP a Katsina ta sanar da kuɗin form ɗin takarar shugabannin ƙananan hukumomi da kansiloli a zaɓe mai zuwa Babbar jam'iyyar adawa a jihar...

Aisha Buhari Ta Naɗa Kashim Shettima A Matsayin Shugaban Kwamitin Amintattu Na Kwalejin Future Assured

Uwargidan Shugaban Ƙasa, Aisha Buhari, ta naɗa Kashim Shettima, tsohon gwamnan Jihar Borno, a matsayin shugaban kwamitin amintattu na Kwalejin Future Assured da ke...

WHICH PARTS OF NIGERIA ATTRACTED MORE FOREIGN INVESTMENTS IN THE YEAR 2021?

https://www.facebook.com/101788642037662/posts/262020019347856/

AGAIN, A NEW ADDITION TO NIGERIA’S MARITIME SECURITY VESSELS!

https://www.facebook.com/101788642037662/posts/261866049363253/

Jami’an Hukumar yaƙi da yima Tattalin Arzikin ƙasa Ta’annuti ta ICPC sunyi Dirar Mikiya jihar Katsina….

Jami'an Hukumar sun gano yadda akayi Haɗin baki da Ɗan Majalisar Wakilai da kuma Mai duba ƙwangila aka sace kuɗin ƙwangilar Naira Milyan Talatin...