Baza a daina kashe yan Arewa ba a karkashin mulkin Buhari__Nastura Ashir sheriff.

Daga Kabiru Ado Muhd

Shugaban gamayyar cigaban kungiyoyin Arewa Alhaji Nastura Ashir sheriff yace baza adaina kashe yan Arewa ba a kudancin Nigeria a karkashin mulkin Buhari.

Alhaji Nastura Ashir sheriff ya bayyana cewa wannan wata dama CE yan kudu suka samu har suke kisan kiyashi akan yan Arewa a jihohin su.

Nastura Ashir sheriff yakaraa da cewa saboda imanin da yan kudu suke dashi cewa babu abinda zaifaru don sunyi kisan kiyashin kan yan Arewa a karkashin mulkin Buhari.

Shugaban gamayyar kungiyoyin Arewa Alhaji Nastura Ashir sheriff yace saboda tsabar rashin martaba rayukan yan Arewa da gwamnatin Buhari keyi yajanyo hakan.

Alhaji Nastura ya bayyana haka ne a lokacin dayake zantawa da manema Labarai a Kaduna dangane da halin da yan Arewa suka tsinci Kansu Na kisan kiyashin da ake musu yanzu haka a sashin kudancin Nigeria musamman jihohin yarabawa.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here