Gwamna Wike ya ziyarci dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar APC Gwamna Yahaya Bello

Daga: Umar Umar Jabo

Ga dukkanin alama dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar PDP kuma Gwamnan jihar Rivers Nyesome Wike na shirin barin jam’iyyar PDP zuwa jam’iyyar APC.

A yau Laraba, Gwamna Wike ya ziyarci takwaran sa dan takarar shugaban kasa a jam’iyyar APC Gwamna Yahaya Bello.

Tun ba yau dai Gwamna Wike ya lashi takobin lallai doli ne dan takarar shugaban kasa ya fito daga kudancin Najeriya a jam’iyyar PDP ko kuma jam’iyyar ta watse.

To sai dai dukkanin alamomi sun nuna cewa da wahala dan takarar shugaba a jam’iyyar ta PDP.

Gwamna Wike dai yana daga cikin jiga-jigan jam’iyyar PDP wadanda idan su ka fice jam’iyyar zata samu gagarumar matsala a zaben 2023.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here