Dan takarar gwamnan jihar katsina a shekarar 2023 karkashin Jam’iyyar PDP Honorabul Salisu Yusuf Majigiri ya halarchi zaman da Jam’iyyar PDP katsina ta kira karkashin jagorancin mataimakin shugaban jam’iyyar na jiha, Honorabul Salisu Uli, inda aka yi zama da Ciyamomi da Kansiloli na Kananan hukumomin jihar baki daya a yau juma’a.

Yayin zaman, an tattuna muhimman batutuwa wadanda suka shafi hanyoyin da za a bi domin tabbatar da kwato wa Ciyamomi da Kansoli hakkinsu, bisa zargin da suke yi na cewa jam’iyya mai Mulki ta APC ta ci masu zalin a yayin gudanar da za6ukan.

Indai ba a manta ba a ranar Litinin din nan ne aka gudanar za6en Ciyamomi da Kansilolin Jihar ta Katsina, inda Jam’iyyar APC ta lashe kusan dukkanin kujerun kananan hukumomin jihar kashin 99%, a yayin da jam’iyyar adawa ta PDP ta tashi 1% kacal.

Hotuna:
Comrades Yusuf Lawal Mai-Iyali

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here