BAYAN SHEKARU HUDU: Za’ayi hawan Salla a Katsina.

Kamar yanda takardar take yawo a Kafafen sada zumunta, wanda kuma Jaridun Katsina City News suka tabbatar da sahihancin takardar ta bakin Sarkin Labarun Sarkin Katsina, cewa;

Takardar mai kwanan wata 25 ga watan Afrilu tana kunshe da sako kamar haka; “Bayan gaisuwa mai yawa da fatan Alkhairi, Mai martaba Sarkin Katsina Alhaji (Dr.) Abdulmumini Kabir Usman CFR ya umarceni da in sanar da ku cewa, in Allah ya yarda za’ayi hawan salla karama wadda ake sa ran za’ayi ranar Lahadi 1/5/2022 ko kuma Litanin 2/5/2022 in Allah ya kaimu.”

Sanarwar ta kara da cewa “Don haka yana so kuzo ranar Asabar 30/4/2022 a fadarsa da karfe goma na safe domin sauraren jawabinsa.” Da fatan Allah ya bamu lafiya da zama lafiya amin. Wassalam.”

Sa hannu daga (ALH. BELLO M. IFO) Sarkin yaƙi.

Kimanin shekaru uku baya Masarautar ta dage hawan Sallah saboda yawan sace-sace da garkuwa da mutane da ake a wasu yankunan jihar Katsina, inda Sarkin yace “ya dauki shawarar Gwamnati da hukumomin Tsaro” a shekarar dubu biyu da ashirin ne Cutar Covid 19 (Mashaƙo) ta gallabibduniya inda ta shafi kusan dukkanin sassan Najeriya wanda shima yana daya daga cikin abinda ya kawo cikas ga wasu taron bukukuwa a fadin Najeriya.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here