Hukumar Daƙile Safarar Ɗan’adam, NAPTIP ta samu danƙa wata yarinya ƴar shekara 5 da haihuwa a hannun iyayenta.

Darakta-Janar ta NAPTIP, Fatima Waziri-Azi, a yayin miƙa yarinyar ga iyayenta a shelkwatar hukumar da ke Abuja a jiya Talata, ta ce an sace yarinyar ne a jihar Gombe, in da a ka sayar da ita a Jihar Anambra.

Ta ƙara da cewa haka iyayen ƴar su ka bazama neman ta amma ba a samu ganin ta ba.

A cewar Waziri-Azi, lokacin da iyayen ƴar su ka kawo rahoton ɓatan nata ga NAPTIP, sai hukumar, da haɗin gwiwar jami’an Ƴan Sandan Farin Kaya su ka riƙa bibiyar wadanda su ka sace yarinyar har ta kai ga an ceto ta an kuma kame masu garkuwar da ita.

Ta kuma yabawa mahaifin yarinyar sakamakon jajircewa da ya yi har sai da a ka gano ƴar ta sa.

Shima mahaifin yarinyar ya yi godiya ga NAPTIP a bisa jajircewa har a ka gano ƴar ta sa.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here