Bayan Makwafcinsa Ya Taimaka Masa Da Dubu 300, SA Galadima Ya Sace Tare Da Kashe Masa Yaro

Bayan karbar kudin fansa har Naira Miliyan biyar a wajen makwafcinsa, sai ya kashe yaron don ya gane daya daga cikin su wanda ya sace shi.

Wani korarren soja mai suna SA Galadima ya sa wani matashi ya sace dan makwocinsa wanda bai kai shekaru goma sannan ya nemi makwacin ya biya kudi inda ya biya Naira Miliyan biyar amma daga bisani, As Galadima ya kashe yaron.

Da ya ke amsa laifinsa a wajen tuhumar ‘yan sanda, korarren sojan ya ce ya kashe yaron ne don ya gane daya daga cikin su watau wanda ya sace shi wanda shima matashin makwacin su yaro ne.

Majiyar Zuma Times Hausa ta ce, a lokacin da AS Galadima ya taba fada da ‘yan sara a Kaduna har suka yanke shi a hannu, uban wannan yaron ne ya ba shi Naira dubu dari uku don ya je asibi niman lafiyarsa.

Fatanmu, Allah Ya jikan wannan yaro, Ya ba iyayensa dangana, Ya yi wa kowa tsari da mugayen makwabta da makusanta.
©Zuma Times Hausa

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here