Advert
Home Sashen Hausa Batun shugabancin APC a Sokoto, Jam'iyyar ta sasanta kanta

Batun shugabancin APC a Sokoto, Jam’iyyar ta sasanta kanta

JAM’IYYAR APC A JIHAR SAKKWATO TA YI MATSAYA KAN ZABEN SHUGABANNIN TA TA HANYA SASANTAWA:

Jam’iyyar APC reshen Jihar Sokoto, ta bayyana cewa ta yi matsaya kan zaben shugabannin ta a matakin Jiha ta hanyar sasantawa.

Shugaban rikon kwarya na Jam’iyyar Alh Isah Sadiq Achida shi ne ya sanar da hakan a jiya Jumu’a a wurin taron masu ruwa da tsaki ga sha’anin tafiyar da Jam’iyyar.

Isah Sadiq Achida ya kara da cewa, a Jihar Sokoto APC guda ce dake magana da yawu guda karkashin jagorancin shugaban tafiyar Maigirma Sanata Aliyu Magatakarda Wamakko Sarkin Yamman Sokoto.

Shugaban da aka turo sakkwato domin Sanya ido da yadda zaben zai gudana, Alh. Sulaiman Usman, ya bayyana cewa an turo su ne domin su gudanar da zaben kamar yadda tsarin Jam’iyyar ya bayyana a cikin ka’idojin zaben.

Ya yabawa jagoran Jam’iyyar a Jihar Sokoto Sanata Aliyu Magatakarda Wamakko kan kokarin sa na rike Jam’iyyar izuwa yanzun nan.

Da suke magantawa, Sanata Ibrahim Abdullahi Gobir da Dan Majalisar wakilai na kasa Hon. Ahmad Abdullahi Kalambaina da Hon. Bello Idris Chimmola dan Majalisar Dokoki ta Jihar Sokoto, wadanda suka Maganta Amadadin mambobin majalisun na APC a kasa da Jihar Sokoto, Duk sun aminta da matsayar da aka cimma na yin zaben ta hanyar sasantawa kamar yadda yake jam’iyyace.

Shugaban kwamitin Dattawa na Jam’iyyar a Jihar Sokoto Alh. Abdullahi Aminu Tafida ya bayyana goyon bayan su kan Wannan matsayar da aka cimma.

Ministan Lamurran Yan sanda Alh Muhammadu Maigari Dingyadi Katukan Sokoto ya ce Jam’iyyar APC a Jihar Sokoto tana nan matsayin tsintsiya madaurinki daya.

Ya bayyana cewa APC sai kara karfi take Musamman a Jihar Sokoto abin da hakan ke nuna nasarar Jam’iyyar a gaba.

Jagoran Jam’iyyar APC na Jihar Sokoto Sanata Aliyu Magatakarda Wamakko Sarkin Yamman, ya bayyana cewa tun shekarar 2014 Jam’iyyar APC take a matsayin Yar Gida daya sannan tana nan daram sai abin da ya ce gaba na samun magoya baya.

Ya yabawa jagorancin Jam’iyyar a matakin kasa kasancewar sun rike kambun ta yadda ya Kamata.

Sanata Wamakko ya bada tabbacin ci gaba da goyon bayan sa ga tafiyar da Jam’iyyar a dukkan matakai.

Taron na Masu ruwa da tsaki ya sami halartar sakataren zartarwar Asusun amintattu na Yan sanda Alh Ahmad Aliyu Sokoto FCNA da jagoron Majalisar Dokoki ta Jihar Sokoto Hon Bello Isah Ambarura, da tsohon Ministan Hon. Yusuf Sulaiman da Hon. Bello Idris Gada da Ambasada Abubakar Shehu Wurno da Ambasada sahabi Isah Gada mni, da Sanata Salihu Bakwai sabon Birni da shugabannin Jam’iyyar APC a matakin kananan Hukumomin Sokoto 23 da sauran mambobin Jam’iyyar da Masu fatan alheri.

Yau Assabar ne dai za a gudanar da zaben a Sakatariyar Jam’iyyar dake kan titin Sarkin Musulmi Abubakar III sake sakkwato.

Labari: Bashar Abubakar MC/Mataimaki na Musamman ga Sanata Aliyu Magatakarda Wamakko kan kafar watsa labarai ta zamani.

Assabar:16/10/2021

KATSINA CITY NEWShttps://www.katsinacitynews.com
Danjuma Katsina, Dan Jarida, Manazarci, Marubuci, Mamallakin Jaridun KATSINA CITY NEWS, JARIDAR TASKAR LABARAI, THE LINKS NEWS, a karkashin Kamfanin MATASA MEDIA LINKS NIGERIAN LTD

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Must Read

WATA SABUWA: Kotu a jihar Gombe ta ci saurayi tarar Miliyan 2.6 saboda yaki auren budurwar sa

Daga: Yushau Garba Shanga Wata kotun majistiret da ke da zama a Kumo fadar ƙaramar hukumar Akko a jihar Gombe ta yanke wa wani matashi...

Rundunar Yansanda Ta Jihar Katsina Ta Chafke Daya Daga Cikin Yan Bindiga Da Suka Hallaka Hakimin Yantumaki.

Rundunar Yansanda ta Jihar Katsina ta samu nasarar chafke daya daga cikin Yan Bindiga da suka hallaka Tsohon Hakimin Yantumaki Marigayi Abubakar Atiku Maidabino,mai...

THE DUALIZATION OF THE IBADAN – ILORIN EXPRESSWAY AND SECTION II OF THE OYO – OGBOMOSO ROAD BY THE BUHARI ADMINISTRATION IS ALMOST DONE!

#PositiveFactsNG In staying true to its passionate commitment to developing Nigeria's infrastructure, do you know that the dualization of the Ibadan - Ilorin Expressway as...

THE APAPA – OSHODI – OWORONSHOKI EXPRESSWAY IS SET FOR COMPLETION AND COMMISSIONING!

https://www.facebook.com/Do-You-Know-NG-101788642037662/ THE APAPA - OSHODI - OWORONSHOKI EXPRESSWAY IS SET FOR COMPLETION AND COMMISSIONING! #PositiveFactsNG Do you know that the reconstruction project of the Apapa - Oshodi...

Kungiyar Mafarauta ta Najeriya HCN ta Karrama Mataimakiyar shugaba ta ƙasa

Kungiyar Mafarauta ta Najeriya HCN ta Karrama Mataimakiyar shugaba ta ƙasa Zaharaddeen Ishaq Abubakar @Katsina City News 6/12/2021 Kungiyar Mafarauta ta Najeriya, wato Hunters Council of...