Daga Umar Abdullahi Tata

Sakamakon furucin da nayi na cewa in Allah ya bani damar zama gwamnan jihar Katsina zan tada katanga ta welder daga farkon Jibia zuwa karshen Faskari local government haka kuma in dauka daga farkon Sabuwa local government ta bangaren Dungun Muazu zuwa dogon dawa haka in dauka daga dogon dawa zuwa Gangara ta Funtua local government ya janyo maganganu iri iri. Babban abinda na jima dadi da masoya da wadanda ba masoya ba, in dai Katsinawa ne, a duk irin kalaman su babu mutum daya daya ce ba zan iya ba sai dai ayi wasu kalaman dabam.

Maganar katanga gaskiya ce. NACE ZANYI KATANGA! A fagen na yaki a koda yaushe mataki na farko ga mai neman nasara shine ka gane inda threat din ka take. A wannan yakin, babbar matsalar mu itace kasancewar barayi suna shigo mamu ta hanyoyi daban daban ta Zamfara da jihar Kaduna suzo su kashe na kashewa sannan su saci na sacewa su kama gaban su su koma inda suka fito. Haka ma namu barayin na cikin gida suna samun gudummuwa gaya daga wadannan barayin a irin ta’asar da suke yi mamu a cikin gida yala Allah ta kisa ce ko ta satar Jama’a. Network garesu na taimaka ma junansu a wannan mummunan aikin. Barayin Katsina zasu iya samun gudummuwa daga barayin Niger state, Kebbi state, Sokoto state, Kaduna state da Zamfara state a kowane lokaci.

Hakanan kawai zaka ga mutane a kan babura sun biyo daji da bindigu suzo suyi barna su koma. Baka iya kawo karshen wannan fitinar sai ka dakile entery da exit points na wadannan shakiyyan. Shiyasa zaka ga a saci mutum a Katsina a karbo shi a Zamfara ko Birnin Gwari. They are so connected ta wadannan dazukan da har juye suke baiwa junansu na victims. To sai ayi kaka? Ni dai bani da soja ko dan sandan da zan zaunar a cikin daji don kare afkuwar wannan matsalar. Dole inyi amfani da damar da itace ke gare ni don taimakon al’umma ta.

Dazukan mu are our greatest weakness to dole sai munyi aikin da zai taimake mu koda kuwa zai saba ma normal tunanin mu. Muna da local governments 9 dake makwabta ka da Zamfara da Kaduna state. Tsawon kilometers din da muke magana kwata kwata is 380 kilometers. Ta ya za ace wannan aikin ya gagare mu? Zai yi wahala ace a matsayi na na gwamna zan rasa N200M duk wata wacce zan saka cikin wannan aikin and inshaa Allahu cikin wata shidda mun gama shi.

Yan banga da zan dauka a matsayi border patrol unit dina zan yi masu bariki a kowace farko da karshe na local government din su. Zan basu filin da za suyi noma. Zama ne na dindindin. Kuma bani zan dauke su ba. Kowane local government zamuyi kwamiti na sarakunan gargajiya, malaman addini, jamian tsaro, masu hannu da shuni, matasa da sauran masu ruwa da tsaki su zasu zabo daga cikin mutanen su wadanda zasu yi wannan aikin.

Muddin muka tsare shigowa jihar mu ta ko ina sauran aikin mai sauki ne inshaa allahu. Ga masoyi na al’umma mai kuma tausaya mata addu’a da fatan alkhairi za ayi mani ba tsegumi da cin fuska ba. In kuwa akwai shawarar da tafi tawa sai a bani. Ni dai na san zuwa yanzun duk wanda yake zaton wai jamian tsaro zasu kawo karshen wannan fitinar to akwai bukatar ya canza tunani. Ni na san bani da jamian tsaron da zan zaunar a daji dindindin don wannan aikin to kun ga kau dole mu nemi mafita. Yana daga cikin gurina inshaa Allahu duk wani soja dake cikin wannan hidimar a cikin jihar Katsina sai ya koma bariki don banga alfanun soja a cikin wannan aikin ba. Mutanen nan an san su infact wasu ma suna makwabtaka da inda sojojin nan suke amman zasu shigo suyi barna soja na kallo su koma su kwana gidajen su wai soja yace ba ace ya dauki mataki ba. To meye amfanin shi. Garuruwan duk sun tashi duk da ga soja a wuri sannan ace akwai wani amfanin da suke yi.

ALLAH ka bamu zaman lafia.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here