Advert
Home Sashen Hausa Bashir Nura Alkali ya zama babban sakataren Ma'aikatar Harkokin Jinƙai

Bashir Nura Alkali ya zama babban sakataren Ma’aikatar Harkokin Jinƙai

Bashir Nura Alkali ya zama babban sakataren Ma’aikatar Harkokin Jinƙai

Bashir Nura Alkali ya kama aiki a matsayin sabon Sakataren Dindindin (Permanent Secretary) na Ma’aikatar Harkokin Agaji, Jinƙai da Inganta Rayuwa ta Tarayya.

A wajen bikin karɓar aikin a harabar ma’aikatar, sabon Sakataren Dindindin ɗin ya bayyana jin daɗin sa ga Ministar ma’aikatar, Hajiya Sadiya Umar Farouq, da daraktoci da dukkan ma’aikatan ma’aikatar, saboda kyakkyawar karɓar da aka yi masa tare da shan alwashin bada dukkan gudunmawar da ake buƙata wajen cimma ƙudirorin ma’aikatar.

Alkali ya kuma buƙaci haɗin kan dukkan ma’aikatan wajen takalar ɗimbin ƙalubalen da ke gaban ma’aikatar.

A jawabin sa, darakta mai kula da Ofishin Sakataren Dindindin ɗin, Grema Ali Alhaji, a madadin Minista Sadiya Umar Farouq da kuma daukacin dukkan ma’aikatan ma’aikatar, ya yi wa babban sakataren marhabin da zuwa.

A jawabin sa na miƙa sandar kama aiki a gare shi, Grema ya yi la’akari da cewa an kafa ma’aikatar ne ta hanyar furucin da shigaban ƙasa ya yi a ranar 21 ga Agusta, 2019 kuma ɗaya daga cikin ayyukan da aka ɗora mata shi ne tattaro tare da kula da ayyukan jinƙai da taimakon jama’a a Nijeriya. Ya ƙara da cewa tun daga lokacin da aka kafa ma’aikatar, Minista Sadiya tare da goyon bayan ma’aikatan sun yi aiki tuƙuru wajen tabbatar da cewa an saisaita ma’aikatar a kan turbar gudanar da ayyukan da aka ɗora mata kamar yadda ya kamata.

Ya bayyana cewa wasu daga cikin ƙalubalen da ma’aikatar ta fuskanta da farko sun haɗa da batun kafuwar ta, harkokin gudanarwa da batun kuɗi, kuma ya zuwa yanzu an warware yawancin waɗannan matsalolin ko kuma ana kan warware su.

Ya ce, “Bin tsarin haɗa komai waje ɗaya kuma a zahiri ga kowa wajen gudanar da duk wani aiki ya samu kulawa daga jawadawalin tsarin gudanarwa da ta hanyar daidaita shi da jerin sunaye da ayyukan ma’aikata wanda ofishin Shugaban Ma’aikatan Gwamnati na Tarayya.

Mataimakiyar Darakta a sashen Yaɗa Labarai na ma’aikatar, Madam Rhoda Ishaku, ta ruwaito Grema ya na tabbatar wa da sabon babban sakataren cewa zai samu dukkan tagomashi da tallafi daga kowane ma’aikaci wajen gudanar da aikin sa.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Must Read

DSS SUNA NEMAN MAWAKIN DA YA YI MATAN KANNYWOOD WAKA

Biyo bayan wani korafi da wasu matan Kannywood suka aikewa Shugaban MOPPAN na Kasa, Dr. Ahmad Muhammad Sarari, mai taken: "KORAFIN CIN ZARAFI DA...

MAJIGIRI ZAI TSAYA TAKARAR DAN MAJALISAR TARAYYA A MASHI DA DUTSI.

Mu'azu Hassan  @Katsina City News Akwai yiyuwar Alhaji Salisu Yusufu Majigiri shugaban jam iyyar PDP a yanzu kuma Wanda ya sha kaye a zaben fitar...

GWAMNATIN TARAYYA NA GAB DA KAMMALA AIKIN RUKUNIN GIDAJE NA ZUƁA A BABBAN BIRNIN TARAYYA ABUJA #PositivefactsNG

https://www.facebook.com/102456081968136/posts/pfbid0CHFGJQoDhZJNMacvv6VTib7xu3pTdvGaAWBDHQvjDZ9NbANEivfEgpFSUwT3Nfunl/ Gwamnatin tarayya na yin aiki babu kama hannun yaro domin ganin kammaluwar aikin ginin rukunin gidaje na Zuɓa cikin nasara. Ƙaramin ministan gidaje Alhaji...

THE ONGOING ZUƁA HOUSING ESTATE PROJECT REACHED FINAL STAGE OF COMPLETING #PositivefactsNG

https://www.facebook.com/101788642037662/posts/pfbid02avw79qxwnbnEgbEJqgSHTsMXdPPpMtEqbZfKv9LBUG8RA9UgE4aanNNDv4r7wUmUl/ The federal government is working tirelessly to complete the ongoing project of mass housing estate in Zuba, the honourable Minister of State of Works...

Supreme Court Strikes Out Buhari, Malami’s Suit On Electoral Act

The Supreme Court has dismissed a suit brought against the National Assembly challenging the legality of the controversial section 84 (12) of the Electoral...
%d bloggers like this: