Mai Martaba Sarkin Gaya Dakta Aliyu Ibrahim Gaya ya naɗa Hadimin Shugaban Ƙasa Muhammadu Buhari kan Sabbin Kafafen Yaɗa Labarai Bashir Ahmad memba na Komitin yaɗa labarai a bikin miƙa sandar Sarauta na Masarautar da ke tafe a watan Jainairun sabuwar shekara.

Bashir Ahmad, shi ne ya bayyana hakan a shafinsa na Facebook, kuma ya ce naɗin nasa na nufin zai jagoranci ƙaramin komitin sabbin kafafen yaɗa labarai.

Ya yi alƙawarin yin amfani da ilimin da Allah ya hore masa a fannin sabbin kafafen yaɗa labarai wurin ganin cewa bikin ya ƙayatar kuma ya zama abin kwatantawa.

Ya kuma bayyana cewa, nan gaba kaɗan zai fitar da tsare-tsare da sunayen ƴan Soshiyal Mediya da suka cancanta don bada gudummawa a wanann gagarumin taro.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here