Basarake ya rasa Rawanin sa saboda zargin taimakawa Barayi a Jihar Katsina

Da Duminsa: Masarautar Katsina ta sami Sarkin Pauwa Hakimin Kankara dumu-dumu da hannu wajen taimakawa yan bindiga, ta tsige masa rawani kwatakwata

A labarin dake zowa Katsina Daily Post News yanzun nan da duminsa, Majalissar Sarkin Katsina ta sami Sarkin Pauwan Katsina Hakimin Kankara Alh Yusuf Lawal, da hannu wajen taimakawa yan bindiga, a don haka ta kore shi kwatakwata daga kujerar da yake bisa kai ta saratau a masarautar.

Za a iya tuna cewa a kwanaki ne dai Katsina Daily Post News ta wallafo maku labarin dakatar da Hakimin da masarautar Katsina ta fara yi sakamakon, zarginsa da taimaka wa yan bindiga masu kai hare-hare a jihar ta Katsina

Sakataren fadar masarautar Katsina, kuma Sarkin Yakin Katsina Alh Bello Mamman Ifo shi ne ya tabbatar da labarin hakan, ga Yusuf Ibrahim Jargaba, shi kuma ya tabbatar mana da faruwar lamarin.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here