Ɗan majalisar tarayya mai wakiltar kananan hukumomin Koko Besse da Maiyama a jihar Kebbi, ya rabawa Sarakunan mazaɓarsa motoci guda goma ƙirar Honda CRV.

Majiyarmu ta Daily Independent Hausa 24 ta rawaito cewa kimanin Hakimai tara ne dake mazaɓar ɗan majalisar suka karɓi kyautar motocin da aka raba musu.

Sai dai a gefe Sarkin Koko Mallam Bello Muhammadu wanda suke mazaɓa ɗaya da ɗan majalisar yaƙi karɓar kyautar motar da akai masa.

Tun da farko dai iyayen ƙasa guda tara ne suka fito daga mazaɓar ɗan majalisar waɗanda suka haɗa da Sarkin Maiyama da Uban ƙasar Andarai da Sarkin Sambawa.

Sauran sune Sarkin Garin Mungadi da Sarkin Garin Maiyama da kuma Sarkin Garin Besse da Sarkin Koko da Uban ƙasar Dutsin Mari da Uban ƙasar Zariya da Uban ƙasar Lani duk sun yi habzi da kyautar motocin da aka yi musu.

Amma a gefe guda Wakilin Mai Martaba Sarkin Gwandu ne ya jagoranci bikin rabon motocin da aka yi a mazaɓar ɗan majalisar a watan Ramadan da muke ciki.

Sai dai har yanzu ba a san dalilin da ya hana Mai Martaba Sarkin Koko Mallam Bello Muhammadu ƙin karɓar kyautar motar da dan majalisar ya yi masa ba.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here