Advert
Home Sashen Hausa Barcelona ta ruga kotu don dakile kulla yarjejeniyar PSG da Messi

Barcelona ta ruga kotu don dakile kulla yarjejeniyar PSG da Messi

Barcelona ta ruga kotun hukumar gudanarwar kungiyar tarayyar Turai EU, inda ta mika bukatar hana kungiyar Paris Saint-Germain kulla yarjejeniya da tsohon kaftin dinta Lionel Messi.

Fitacciyar jaridar wasanni ta Marca da ke Spain, ta ruwaito cewa lauyan Barcelona Juan Branco ne ya shigar da karar gaban kotun da ke birnin Paris.

Babbar hujjar da Barcelona ta gabatar cikin korafin nata shi ne yadda PSG ke shirin karya dokar da ke haramtawa kungiyoyi kashe kudade fiye da abinda suke samu da aka fi sani da ‘Financial Fair Play Rule’ a turance, la’akari da manyan ‘yan wasan da ta saya a baya bayan nan da suka hada da Sergio Ramos, Wijnaldum, Achraf Hakimi, Gianluigi Donaruma, ga kuma albashin Neymar da Mbappe ‘yan wasa mafiya tsada da take da su, baya ga Messi da ake sa ran yana tafe.

Tun a ranar 1 ga watan Yuli Messi ya kasance dan wasa mai zaman kansa abinda ya sa PSG ba za ta bukaci biyan Barcelona ko da sisi ba kan kulla yarjejeniya da shi.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Must Read

Shugaba Buhari ya nemi kasashen duniya su yafewa Najeriya bashin da suke binta

A yayin da yake gabatar da jawabi a zauren majalisar dinkin duniya a ranar Juma'a. Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya nemi manyan kasashen duniya...

Bangaren aikin jarida na H.U.K Poly sun yaye kwararrin ‘yan social media a Katsina

Bangaren aikin jarida na H.U.K Poly sun yaye kwararrin ‘yan social media a Katsina Saifullahi Kuraye‎ September 24, 2021 2 min read Bangaren aikin jarida na...

Hukumar Hana Fasa ƙwabri ta ƙasa wato Custom ta ƙwato Babura Ɗari Biyu da Biyu a Jihar Katsina…

Shugaban Hukumar Ƙwastam na Jihar Katsina Mr. Chedi ne ya bayyana hakan ne a Yau Juma'a cewa tsakanin watan Agusta zuwa Satumba Hukumar ta...

Dan Najeriya ya fiye tsogwami: da ₦500 kacal sai aci a ƙoshi……Inji farfesa Segun Ajibola

Da Naira Dari Biyar ( 500 ) kacal Zaka Iyaci Ka Koshi a Najeriya, Cewar Wani Farfesa, Masanin Tattalin arziki... Tsohon shugaban kwalejin ma'aikatan bankin...

Rail project will not displace host communities-FG

Radio Nigeria The Federal Ministry of Transport and that of Environment have given assurance to residents along the proposed stretch of land demarcated for the...
%d bloggers like this: