Yanzu-yanzu: An haramta zanga-zanga a birnin tarayya Abuja
Ministan birnin tarayya Abuja, Malam Muhammad Musa Bello, ya haramta zanga-zanga birnin kuma ya yi hakan ne saboda matasan dake rajin kawo karshen zalunci da zarafin da yan sanda ke yiwa yan Najeriya wanda aka yiwa take #ENDSARS.
A jawabin da hukumar birnin tarayya FCTA ta saki, kwamitin tabbatar da tsaron Abuja ta haramta zanga-zanga inda tayi zargin masu yi da sabawa dokokin COVID-19.