Barawon Motar Gwamnati Ya Shiga Hannu A Katsina.

Rundunar Yan Sanda ta Jihar Katsina ta samu nasarar chafke wani mai suna Hayatu Bishir da ake zargi da sace wata mota kirar Hilux mallakin Ofishin Sakataren Gwamnatin Jihar.

Wanda ake zargin dai ya sace motar ne a Masallacin Juma’a na GRA dake Katsina tare da gudummuwar abokan sana’arsa ta sace-sacen motoci.

Kakakin Rundunar S.P Gambo Isah ne ya gabatar da wanda ake zargin ga manema labarai a Ofishin Yansanda na Sabon Gari dake cikin Birnin Katsina.

Kamar yadda SP Gambo Isah ya bayyana,an chafke Wanda ake zargin ne a kusa da garin Dayi na Karamar Hukunar Malumfashi a dai-dai lokacinda yake yunkurin batar da motar daga Jihar Katsina.

Yace bayan sanar da Rundunar akan lamarin sace motar jami’anta suka tsunduma ka’in da na’in ta hanyar amfani da fasahohi na zamani wanda hakan ya bada damar chafke Wanda ake zargin.

Kakakin Rundunar ya tabbatar da cewa Wanda ake zargin ya shahara wurin satar motoci wanda wannan shine karo na uku da shi kanshi ya gabatar da Mai laifin ga Yan Jarida akan laifi iri Daya.

Sai dai da yake amsa tambayar manema labarai,Wanda ake zargin Hayatu Bishir yace wani mutum ya aikeshi da motar zuwa Zaria a Jihar Kaduna.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here