Daga Auwal Isah da Ibrahim Tukur Garkuwa

Matasan jam’iyyar APC a karamar hukumar Dutsin-ma, sun koka kan yadda harkokin jam’iyyar APC ke neman sukurkurcewa a matakin karamar hukuma.

Shugaban kungiyar ‘Coalition Of All APC Youth Dutsin-ma Local Government’ a turance, Ahmad Tijjani Ahmad ne ya yi wannan koken a yayin da yake kar6a tambayoyin ‘yan jarida kan hadin kan matasan jam’iyyar ta APC na Dutsin-ma a ranar Litinin din nan.

“Babban abin da ya jawo hankalinmu a kan kafa wannan kungiya shi ne ganin irin yadda jam’iyyarmu ta APC ta samu tasgaro a za6en da aka gudanar na kananan hukumomi a karamar hukuma Dutsin-ma da aka yi.” In ji shi.

“Wannan dalilin ne ya sanya muka ga a matsayinmu na matasa, ya kamata a ce mun yi wani gangami don mu gane daga ina matsalar take, da kuma yadda za a yi mu magance wannan 6araka da take shirin afkuwa a cikin wannan jam’iyya tamu a karamar hukumar Dutsin-ma.” Ya koka.

A ranar 11 ga watan Afrilun nan ne dai aka gudanar da za6ukan Ciyamomi da Kansiloli na kananan hukumomin jihar Katsina, inda jam’iyyar APC ta samu nukushin bayyana sakamakon za6en tare da soke shi, sakamakon zargin da jam’iyyar ta APC ke yi ga jam’iyyar adawa ta PDP na tada hargitsi da hana wasu za6uka a wasu rumfunan za6e a karamar hukumar.

Yanzu dai kallo ya koma sama kan yadda masu ruwa da tsaki na jam’iyyar za su dauki matakin sukurkucewar jam’iyyar da Matasan ke koken faruwa. A 6angaren hukumar za6e kuma, shi ma mun zura na mujiya domin mu ga fasalin da ta canja kan aiwatar da wani sahihin za6en.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here