Bankin Duniya ba zai ba Najeriya rance ba sai darajar naira ta farfaɗo’

Bankin Duniya ya ce sai Najeriya ta ƙara ƙarfafa matakan farfaɗo da darajar naira kafin ya amince da rancen dala biliyan 1.5 da ƙasar ke buƙata.
Daraktan Bankin Duniya a Najeriya ne Shubham Chaudhuri ya bayyana haka a ranar Alhamis yayin da dala ke ci gaba da wahala a kasuwa, kamar yadda kamfanin dillacin labarai na Reuters ya ruwaito
A watan da ya gabata an sayar da dala kan kusan naira 500 a kasuwar bayan fage.
Najeriya ta nemi rancen ne domin farfaɗowa daga matsalar tattalin arziki da annobar korona ya haifar da kuma faɗuar farashin ɗanyen mai a kasuwa.