Advert
Home Sashen Hausa BANKIN CBN ZAI KADDAMAR DA TSARIN BAYAR DA TALLAFI MAI TAKEN "100...

BANKIN CBN ZAI KADDAMAR DA TSARIN BAYAR DA TALLAFI MAI TAKEN “100 FOR 100 PPP”_____EMEFIELE

Babban bankin Najeriya wato CBN zai kaddamar da wani sabon tsarin bayar da tallafi ga kamfanoni 100 cikin kwana 100 mai taken “100 for 100 PPP domin fadadawa tare da inganta kayayyakin da su ke sarrafawa wanda hakan zai taimaka wajen farfado da harkokin kasuwanci da tattalin arzikin Kasa.

Gwamnan CBN Godwin Emefiele ne ya sanar da hakan a lokacin bikin kaddamar da sabon tsarin nan na kudin yanar gizo wato enaira.

Emefiele ya ce tsarin wata hikima ce ta zabar kamfanoni 100 cikin kwanaki 100 domin basu tallafin da zai inganta harkokin su na sarrafe-sarrafe da nufin rage yawan dogaro da kayayyakin kasashen ketare.

Emeifele yace, za a cigaba da gudanar da Shirin ne daga sashen bayar da tallafin kudade kuma karkashin kulawarsa.

kuma ba a kan kamfanoni 100 kaɗai Shirin zai tsaya ba, inda bayan cikar kwanaki 100, za a sake zaba tare da tantance wasu kamfuna 100 domin bayar da tallafin. Sai dai Emefiele yace, za a fara Shirin ne a cikin wannan wata na nuwamba kuma za a wallafa sunayen kamfanonin da za a ba tallafin a shafukan jaridun kasar nan domin samun tantancewa da Kuma gani-da-idon yan’ najeriya.

Yace, bankin zai yi aiki ta hanyar bankunan kasar nan domin samar da tallafi ga kamfanonin domin inganta ayyukan su na sarrafe-sarrafen kayan cikin gida domin bukatun yan’ najeriya.

CBN ta sha ƙaddamar da shirye-shirye masu yawa domin bunƙasa tattalin arziki a fannonin noma, kiwo, kasuwanci, hada-hada da sauran su.

Ko a makon da ya gabata sai da CBN ya ƙaddamar da shirin bayar da lamuni ga ɗaliban da su ka kammala karatun digiri na farko da Difiloma, waɗanda ke da sha’awar kama kasuwanci.

KATSINA CITY NEWShttps://www.katsinacitynews.com
Danjuma Katsina, Dan Jarida, Manazarci, Marubuci, Mamallakin Jaridun KATSINA CITY NEWS, JARIDAR TASKAR LABARAI, THE LINKS NEWS, a karkashin Kamfanin MATASA MEDIA LINKS NIGERIAN LTD

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Must Read

THE FEDERAL MORTGAGE BANK OF NIGERIA (FMBN) HAS MADE HISTORY UNDER THE BUHARI ADMINISTRATION!

#PositiveFactsNG Do you know that ever since the Federal Mortgage Bank of Nigeria (FMBN) was established about 25 years ago, its greatest record of achievement...

YANZU-YANZU | Jirgin ruwan Bagwai dake jihar Kano mai dauke da fasinjoji 40 Yayi hatsari

Jirgin ruwan wanda ya debo dalibai mata da maza daga garin Badau zuwa garin Bagwai a jahar Kano yayi hatsari a cikin ruwan Yanzu...

ALLAH SARKI: ALLAH KA RABA MU DA RANAR NADAMA

Danjuma katsina  @Katsina City News A shekarar 2000 na dawo Katsina da zama, bayan shekaru na gwagwarmaya da tsallake siratsai kala-kala. Bayan na dawo na tsara...

Yadda Kotu Ta Ruguza Zaɓen Bangaren Ganduje Na Jam’iyyar APC

Wata babbar kotun Abuja ta soke zaben shugabannin jam'iyyar APC bangaren gwamnan jihar Kano Abdullahi Umar Ganduje. Alkalin kotun Hamza Muazu ya haramta zaben da...

EFCC Charges Corps Members To Take CDS More Seriously

The Port Harcourt Zonal Commander of the EFCC, Assistant Commander of the EFCC, ACE Aliyu Naibi has called on members of the National Youth...