Daga Usman Salisu Gurbin Mikiya

Gwamnan Jahar Katsina, Alhaji Aminu Bello Masari ya sake jaddada kudirin sa cewa bai da wani dan takara a kowace kujera, wanda yake da kudirin ya gaje shi a zaben Shekarar 2023.

Gwamnan ya bayyana hakan ne lokacin da yake jawabi a wurin taron masu ruwa da tsaki na jam’iyyar APC, Wanda ya gudana ranar Litinin a Dakin taro na gidan Gwamnatin Jahar.

Kamar yadda Gwamnan ya bayyana, yace zai kara azama domin ganin an tabbatar da Adalci ga kowa, inda ya bukaci Yan takara dasuje su nemi Jama’a a zaben da zaizo.
Gwamnan ya umarci kowace karamar hukuma, data kawo sunayen wadanda zasu shugabanci jam’iyyar a zaben da za’a gudanar na Jami’iyyar.

Acewar sa, akwai bukatar ayi sasanci a tsakanin Yan takarar Shuwagabancin Jami’iyyar, amma idan ya gagara sai a gudanar da zabe.

Taron ya samu halartar manya-manyan masu ruwa da tsaki na Jami’iyyar APC na Jahar Katsina.

Dimokradiyya.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here