Bangaren aikin jarida na H.U.K Poly sun yaye kwararrin ‘yan social media a Katsina

Saifullahi Kuraye‎ September 24, 2021 2 min read

Bangaren aikin jarida na Makarantar kimiya da Fasaha ta Hassan Usman Katsina Polytechnic, Katsina sun yaye Daliban farko da suka samu horo kan, kafar sadarwa ta zamani “social media”.

An gudanar da taron ranar Juma’a 24/9/2021,a dakin taro da harabar makarantar. Mahalarta taron sunyi fatan alheri ga wadanda suka samu horon, sun kuma yi fatan suyi amfani da abinda aka koyar dasu ta hanyar da zai amfanesu ya kuma amfani Al’umma baki daya.

Da yake jawabi mai baiwa Gwamna Shawara akan harkokin siyasa, Hon. Kabir Shu’aibu Charanci, ya bayyana cewa” wannan shirin bada horo zai cigaba, tare da bullo da wasu tsare, tsare domin ganin an tsabtace harkar “social media” a Jihar Katsina, yadda Matasa masu amfani da ita zasu maidata, abunyi ba hanyar cin mutuncin juna ba.

Haka kuma, Shugaban shahararren Kamfanin, kafar sadarwa ta zamani “Mobile Media Crew” Abubakar Shafi’i Alolo ya bada sanarwar daukar ma’aikata, daga cikin wadanda suka samu horo akan “Social Media” shirin da Gwamnatin Jihar Katsina, karkashin Jagorancin Rt.Hon.Aminu Bello Masari CFR ta dauki nauyi.

Ya sanar da hakan lokacin da ake bada takardar shedar samun horo akan kafar sadarwa ta zamanin wato “Social Media” a makarantar Hassan Usman Katsina Polytechnic.

Inda yake cewa “Harkar social media, wata hanya ce ta dogaro dakai, amma ga wanda ya riketa da Mahimmanci. Samun wadanda suke da horo akan “Social Media” ya bamu kwarin gwiwar kara daukar ma’aikata, a cikin masana’antarmu ta yada labarai bisa yanar gizo. Saboda duk abinda kake da ilmi kanshi, zaka tafiyar dashi bisa tsarin doka da ka’idoji.”

Shugaban ya godema Mai girma Gwamnan Jihar Katsina Rt. Hon. Aminu Bello Masari, akan daukar nauyin bada horon ga masu amfani da kafar sadarwar zamani “Social Media” a Jihar ta Katsina.

Taron ya samu halartar Shugaban Makarantar Kimiyya da Fasaha ta Hassan Usman Katsina Polytechnic, Dr. Mudi Kurfi wanda ya samu wakilcin mataimakinsa, Mai baiwa Gwamna Shawara akan Harkokin siyasa Hon. Kabir Shu’aibu Charanci, Dr. Bashir Kurfi, Malamai daga sashen koyar da aikin Jarida na Makarantar Dr. Mukhtar El-Kasim da Dr. Sama’ila Balarabe wanda sune suka kai gauro suka kai mari har wannan bada horo ya tabbatar cikin nasara.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here