Daga Mannir Ibrahim mashi.

Da farko muna yi ma Sen Ahmed Babba Kaita ban gajiya da zuwa daurin auren diyar shi Maryam Mannir Talba. Bayan haka muna jajanta mashi bisa cin fuska da wasu suka yi mashi a wurin daurin auren. A bisa binciken da muka yi babu dan Mashi a ciki mun gano duk yaran zuwa su kayi, aiko su aka yi daga waje, ina da tabbacin babu dan siyasar garin Mashi da zai sa ayi haka a gidan Iya.

An tabbatar mani cewa wannan abun dama shirya shi aka yi don aci mashi fuska amma mu da muka gayyato shi mu aka muzanta tare da masarautar Mashi karkashin jagorancin Maigirma Iyan Katsina kuma Hakimin Mashi. Sen Ahmed kuma wallahi ko a jikin shi don Allah dai shine gatan shi, mutane kuma sune shaidun shi.

Na biyu ku sani Mannir Talba da Ahmed Babba Kaita tare su ka tashi tun suna yara, saboda haka ba alakar siyasa ko dalilin siyasa yasa Ahmed halartar wannan daurin aure ba. Ahmed dan cikin gida ne a Mashi shi ya sa ma sai da ya shiga har ciki ya gaida tsohuwa.

Na uku ku sani tun jiya Sen Ahmad Babba Kaita ya samu rahoton haka na iya faruwa amma yayi rantsuwa cewa ba abin da zai hana shi halartar auren diyar shi wadda da shi aka auro uwar ta, kuma gaban shi aka haife ta. Dattakun Ahmed ya hana shi bayyana mana hakan sai yau bayan abin ya faru muka ji hakan. Da Allah Ya sa mun ji wallahi dan mutum bai isa ya zo har gidan mu ya ci zarafin bakon mu ba, wallahi ba dai a Mashi ba. Harkar siyasa daban harkar kuma zumunci daban shi ya sa mutane daga kowane fanni su ka zo.

Alhamdulillah kuma taro anyi an gama lafiya kowa ya koma gida lafiya. Allah Ya biya mun gode masu mugun nufi kuma Allah Ya maida masu abin su.
….mannir Ibrahim mashi Dan kasuwa ne kuma Dan siyasa mazaunin Kaduna. Yayi wannan rubutun ne a shafin sa na Facebook.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here