Advert
Home Sashen Hausa BANBANCIN A TSAKANIN SAMMACIN KOTU DA JINGINE WARANTIN KAMO MAHADI DA BINCIKEN...

BANBANCIN A TSAKANIN SAMMACIN KOTU DA JINGINE WARANTIN KAMO MAHADI DA BINCIKEN SA.

BANBANCIN A TSAKANIN SAMMACIN KOTU DA JINGINE WARANTIN KAMO MAHADI DA BINCIKEN SA.
Daga shafin jamilu hassan Dutsinma
Na Facebook
——————————————–

A ranar 26/10/2020, Babbar Kotun Majistare ta daya dake nan Katsina ta bada umurnin a lika samanci a gidaje da wuraren sana’ar Mahadi Shehu don ya zo, ya kare kansa daga tuhumar laifin buga takardun bogi da tunzura jama’a da Gwamnatin Jihar Katsina ta gurfanar da shi a gaban ta.

Sai kuma ga shi a ranar 30/10/2020 Kotun ta ba da wata oda wacce a ciki ta jingine damar da ta riga ta ba yansanda cewa su kamo Mahadi tare da izinin gudanar da bincike a gidansa.

Wannan oda ta biyu ta saka wasiwasi a zukatan wasu mutane don haka suke neman bayani akan me hakan ya ke nufi, a yayin da wasu ma suka soma hangen kamar wanda ake tuhumar ya samu nasara, shi ke nan ba za a iya kama shi ba kuma ba za a ci gaba ma da shari’ar sa ba.

To sam, ba haka abin yake ba, domin Lauyan da ya shigar da kara ta farko Ernest Obunadike ya yi mana karin haske kamar haka:

1. Karar da Gwamnatin Jihar Katsina ta shigar kai tsaye a gaban Kotun wadda ta jaza aka lika sammaci a gidajen Mahadi Shehu tana nan daram, kuma za a ci gaba da ita a ranar Talata, 3 ga wannan watan.

2. Wajibi ne ga Mahadi ya bayyana a gaban Kotun, idan kuma ya ki, kuma ya yi biris da wannan kira, to za a iya cajin shi da laifin raina Kotu, wanda hakan na iya jaza Kotun ta bada umurnin a kamo shi duk inda yake kuma ta aika da shi gidan yari.

3. Kuma, Kotun na iya bada dama ga Lauyan mai kara ya ci gaba da gabatar da tuhumar da ake yi wa Mahadi tun daga farko har karshe, kuma ta yanke hukuncin da zai hau kansa duk ranar da ya saki aka kamo shi.

4. Wannan oda ta biyu an bada ta ne akan karar dake kwamishinan yansanda na Jihar Katsina da Mahadi Shehu kamar yadda za ku iya gani idan ku ka buda takardar odar dake sama don haka wannan ba ta shafi shari’ar farko ba.

5. Ita kan ta odar ba ta din-din-din ba ce, a’a. Kotun ta jingine umurnin yansanda kamo Mahadin ne na wurin gadi har zuwa lokacin da wani Lauyansa ya roki a ba shi dama ya gabatar da wani karfi a gaban babbar Kotun jiha.

Abin mamaki ma shi ne ita babbar Kotun ta ki amincewa da rokon da Lauyan Mahadin ya gabatar na neman ta hana yansanda su kama shi, abinda ita karamar Kotun ta yi, kuma akan karar da ba ma gabanta take ba.

Abin jira a gani shi ne; ko akwai wata kotu ko doka da za ta iya hana Gwamnatin Jihar Katsina ko jami’anta su gurfanar da Mahadi a gaban kotu?

Kuma wane irin raggon azanci ne ga mutumen da ya yi ta cika baki cewa ” idan an isa a kai shi kotu ” yanzu kuma ya koma yana boye-boye? Anya kuwa rayuwa na yiwuwa ta ci gaba a haka, Mahadi?

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Must Read

SHARHIN: Katsina City News ZABEN SHUGABANNIN APC A KATSINA

SHARHIN: Katsina City News ZABEN SHUGABANNIN APC A KATSINA ...A tabbatar Da An Yi Adalci *Jinjina Ga Gwamnan Katsina Da Alhaji Muntari Lawal @Katsina City News Ranar Asabar 2...

Sheikh Zakzaky Meets Families and Survivors of Zaria Massacre

Sheikh Zakzaky Meets Families and Survivors of Zaria Massacre Some families of the those killed by the military in Zaria in December, 2015 met with...

HOTUNA; Malam Ibrahim Zak zaky ya gana da iyalan wadanda suka rasa yan uwansu. Wani hoto da shafin jaridar Al mizan ya fitar ya...

HOTUNA; Malam Ibrahim Zak zaky ya gana da iyalan wadanda suka rasa yan uwansu. Wani hoto da shafin jaridar Al mizan ya fitar ya...

A FIVE DAY OLD BABY, FIVE NURSING MOTHERS AND OTHERS ESCAPED FROM BANDITS’ CAMP

A FIVE DAY OLD BABY, FIVE NURSING MOTHERS AND OTHERS ESCAPED FROM BANDITS' CAMP Hassan Male @Katsina City News Katsina State government has called on the...
%d bloggers like this: