Dan Majalisa dake wakiltar Karamar Hukumar Katsina a Majalissar Dokokin Jiha Alhaji Ali Abubakar Albaba, yace bai taba zuwa da wani kudiri ba a zauren Majalissar wanda ya bi ta gaban Gwamna Masari kuma bai amince da shi ba.

Dan Majalissa Albaba na magana ne a lokacinda yake zantawa da wakilin Jaridar The Fact 24 a Katsina.

Kamar yadda Albaba ya bayyana aikin Gadar Kasa da Gwamnatin jiha ke gudanarwa a halin yanzu, shine kudiri na sama da dubu daya da ya gabatar a zauren Majalissar kuma Gwamna Masari ya amince da shi.

Alhaji Ali Abubakar Albaba yayi magana mai tsawo akan dumbin kudirce-kudirce da ya gabatar a zauren Majalissar kuma Gwamna Masari ya amince da su.

Ya Kara da cewar shi baya iya tuna kudiri daya da ya gabatar Gwamnan bai amince da shi ba.

Kamar yadda ya bayyana,tsakaninshi da Gwamna Aminu Masari sai godiya da kuma addu’a akan Allah SWT ya kara yi mashi jagoranci ta fuskar kawo cigaban Jihar Katsina.

Daga nan sai ya kara jaddada kudirinshi na cigaba da kawo kudurori da zasu inganta rayuwar al’ummar Mazabarshi da ma jiha baki daya.

Ya bukaci al’umma akan kada su gajiya wurin cigaba da addu’oi akan Allah ya kawo karshen matsalolinda ke addabar Jihar Katsina da ma Kasa baki daya domin samun karin cigaba.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here