Karya ne, bamu baiwa Ganduje Farfesa ba, jami’ar East Carolina

Wata jami’ar kasar Amurka, East Carolina ECU, ta karyata nada gwamnan jihar Kano, Abdullahi Umar Ganduje, a matsayin Farfesa mai ziyara.

Jaridar Premium Times ta aike wasika jami’ar ranar Alhamis domin tabbatar da sihhancin labarin nadin Ganduje duk da cewa an kama shi a bidiyo yana karban daloli.

A martanin jami’ar, ta bayyana ainihin abinda ta aikewa Ganduje.

Mukaddashin shugaban jami’ar, Grant Hayes, ne ya rattafa hannu kan wasikar.

Wasikar yace: “Na samu labarin cewa ka samu wasika daga daya cikin mambobin tsangayar mu a ranar 30 ga Nuwamba, 2020, cewa an baka gurbin aiki a cibiyar cigaban ilmin zamani a tsangayar ilmin kasuwanci na jami’ar East Carolina.”

“Ina son sanar da kai cewa wasikar da ka samu daga Dr. Victor Mbarika, ranar 30 ga Nuwamba, bai zo da wani matsayi na gurbin aiki ko nadi matsayin Farfesa daga hukumomin jam’iyar East Carolina ba.”

Dr Abdullahi Umar Ganduje Gwamnan jihar kano

“Cansala kadai, Ni, ko wani sanannan jami’i a sashen karatu zai iya sanya hannu kan takardan bada gurbin aiki. Dr Mbarika bai da irin wannan izini,” wasikar ya kara.

Zaku tuna cewa sakataren yada labarin Ganduje, Abba Anwar, a jawabin da ya saki ranar Talata cewa cibiyar bunkasa fasahar sarrafa labarai ta kasa da kasa a Jami’ar East Carolina da ke kasar Amurka, ta dauki gwamnan jihar Kano, Dakta Abdullahi Umar Ganduje, aiki a matsayin Lakcara.

Jami’ar ta ce ta zabi karrama Ganduje da wannan aiki ne domin samun damar karuwa da dumbin iliminsa, basirarsa, da kwarewa a harkar mulki.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here