Home Sashen Hausa Bama goyon bayan Rufe kafafen sadarwa a Arewa- Inji Dattawan Arewa

Bama goyon bayan Rufe kafafen sadarwa a Arewa- Inji Dattawan Arewa

DA DUMI-DUMIN SU!

“Bamu Goyon Bayan a Rinka Datse Layukan Sadarwa a Arewacin Najeriya Sabida Tsaro, Domin Hakan Zai Tsananta”~Inji Kungiyar Dattawan Arewa

Kungiyar dattawan arewa ta NEF ta ce sanya kulle da kuma katse sadarwa za su kara tsananta rayuwa ne a arewacin Najeriya.

 

A ranar lahadi, kakakin NEF Dakta Hakeem Baba-Ahmed ya ce wannan matakin zai iya tsananta rashin tsaro kamar yadda bayanai suka nunar.

 

A ranar assabar ne, hukumar sadarwa ta NCC ta umarci duk kamfanonin sadarwa su dakatar da sadarwa a jihar Zamfara sakamakon hauhawar rashin tsaro a jihar.

Kungiyar ta dattawan Arewa NEF, ta ce bata goyon bayan wannan matakin domin a cewar ta hakan ba zai samu nasarar samar da tsaro ba.

“Wasu gwamnatin jihohi sun dauki wasu matakai kamar dakatar da kasuwannin makonni, rage yawan fetur din siyarwa, rufe makarantu da wasu titina, sanya kulle dakatar da yawon shanu da kum dakatar da sadarwa a bangarorin da rashin tsaro yafi tsananta duk da halin da suke ciki”

“Sam wannan ba zai taimaka ba wurin kawo dauki ga mutanen da suke cikin tashin hankali irin wannan ba. Ya kamata gwamnati ta kawo wasu hanyoyin da za su taimaka musu ne ba su cutar da su ba”~Inji Kungiyar

Kungiyar ta ce, matakin katse layukan sadarwa a wasu jihohi zai rushe tattalin arzikin mutanen da ‘yan ta’adda suka tasa gaba kuma su dakatar dasu daga sanar da matsalolin su.

Wannan maganar ta dattawan Arewa na zuwa ne daidai lokacin da wasu yan Najeriya musamman yan yankin arewa ke ganin sauyi da kuma nasarar da ake samu a jihar Zamfara sakamakon datse hanyoyin sadarwa da aka yi yanzu haka.

Majiya: Jaridar Sokoto

NO COMMENTS

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

%d bloggers like this: