Badakalar Kudi: Auren diyar Buhari da wanda ICPC ke zargi ya mutu-
DCL Hausa

Garba Shehu da ke magana da yawun shugaban Nijeriya ya ce Gimba Ya’u kumo da hukumar yaki da cin hanci ta ICPC ke nema ruwa jallo yanzu ba surikin Shugaba Buhari ba ne.

A cikin wata sanarwa da Garba Shehun ya fitar a ranar Jumma’a wace majiyar DCL Hausa ta samu ya ce auren da ke tsakanin jami’in da ake zargin da diyar Shugaba Buhari ya jima da mutuwa.

Jaridar Daily Nigerian ta ruwaito Garba Shehu na cewa koda ma auren bai mutu ba Shugaba Buhari kamar yadda kowa ya san shi ba zai bayar da kariya ga duk wani mai laifi ba.

Tun a shekara ta 2016 ne dai aka daura auren da ke tsakanin diyar Shugaba Buharin da kuma wanda ICPC ke nema. Sai dai Garba Shehu bai fadi zahirin lokaci da shekarar da auren ya mutu ba.

ICPC dai na zargin Gimba Ya’u Kumo ne da zambar kudaden da suka kai Dala miliyan 65 kuma hukumar ta ce jami’in ya gudu.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here