Shugaban majaisar malamai na ƙungiyar Izala reshen Jos, Sheikh Sani Yahaya Jingir, yace ba zasu sake yarda yan siyasa su yaudare su ba..

Shikh Jingir ya yi wannan furuci ne yayin da yake wa’azi a wurin wa’azin ƙasa da ƙungiyar ta saba shiryawa, wanda ya gudana a Jingir.

Jingir Ya Kara Cewa ” Kada mu sake mu yarda wani ɗan siyasa ya je ya siyar da kuri’un mu da sunan yarjejeniyar tsarin mulkin karba-karba a babban zaɓen 2023.”

“Wannan tsarin da yan siyasa ke magana a kansa tamkar wata caca ce, kuma yana nufin wasu tsirarun mutane yan siyasa sun maida yan ƙasa tamkar kayan su.”

– Katsina Online

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here