Tsohon shugaban hukumar yaƙi da cin hanci ta Jihar Kano, Muhuyi Magaji Rimingado, ya tabbatar wa BBC Hausa kama shi da ƴan sanda su ka yi amma ya ce ba a faɗa masa laifin da ake tuhumarsa da shi ba.

Ƴan sanda sun kama tshohon shugaban ne wanda ke neman tsayawa takarar gwamnan Kano a babban zaɓe na 2023 a Abuja yayin da ya je aikin tantancewa da jam’iyyar PDP ta shirya.

“Babu wanda ya faɗa min dalilin da ya sa aka kama ni, ba a faɗi wani laifi ba a takardar izinin kama ni,” in ji Muhuyi cikin wani saƙo da ya aike wa BBC.

Wata takarda da aka gabatar wa Muhuyi ta nuna yadda wata kotun majistare a Kano ta ba da umarnin kama shi.

Yanzu haka yana tsare a ofishin ‘yan sanda na Abuja, babban birnin Najeriya.

Gwamnatin Kano ƙarƙshin Gwamna Abdullahi Umar Ganduje ta dakatar da Muhuyi ne daga muƙaminsa bayan zargin sa da badaƙala a wasu kwangiloli da kuma aringizo tare da ƙaddamar da bincike kan sa a watan Yulin 2021.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here