Advert
Home Sashen Hausa Babu Shaidar Chewa Ankashe Ɗan-Bindiga TURJI 'GUDDE'!

Babu Shaidar Chewa Ankashe Ɗan-Bindiga TURJI ‘GUDDE’!

Babu Shaidar Chewa Ankashe Ɗan-Bindiga TURJI ‘GUDDE’!

Tsakanin Sa’a Goma Shabiyu Zuwa Wannan Lokachi Babu Sahihiyar Shaidar Chewa Jami’an Tsaro Sunkai Farmaki a Dabar Ƙasurgumin Ɗan Fashin Dajinnan Mai Suna TURJI.

Bayannun Dana Tattara Daga Magan-ganun Da Nayi Da Mazauna Shinkafi Da Kwaren Zurmi a Chikin Wannan Lokachi, Sun Nuna Chewa BELLO TURJI Shinanan Dabarshi Dake Yamma Ga Ƙasar FAKAI Wadda Wutsiyar Dajin RUGU Che Dake Ƙasar Katsina. Kuma Har Iya Lokachin Wannan Bayani Babu Jami’an Tsaron Da Suka shiga Chikin Wannan Daji Domin Kamashi Ko Yin Faɗa Dashi. Babu majiyar Haƙiƙani Ta Soja Ko Gwamnatin Zamfara Data Fidda Sanarwar Chewa Anyi Faɗa Da TURJI Ko Ankamashi Ko Ankasheshi.

Abunda Zai faru Shine Kafin Akama TURJI Akwai Dabobi Na Ƴan Bindiga Guda Biyu Waɗanda Tabbas Sai Anchi su Da Yaƙi Kafin Akai Dabar TURJI.

*Akwai Dabar ƊAN BOKKOLO Wanda Tananan Zanfarta Ga ƘURYAR DANBO Ƙarƙashi Riƙon Zurmi. Ɗan Bokkolo Yaron Turjine. Commander Ne Chikin Commanders Na Turji. Shima Yimai Laƙabi Da Garkuwa.

*Akwai Dabar BUZU Tananan Arewachin Dajin Ƙursasa. Wanda Wannan BUZU Da Yaranshi ne Suke kai Samame Yankin Shinkafi Da Gabaschin Sokoto Ta Ƙasar Isa Da Gobir. Yana yimai Laƙabi Da Harsashe.

Kuma Waɗannan Dabobi Sunanan Da Ƙarfinsu Hasali ma Achikin Wannan Satin Ansache Mutane Daren Alhamis Garin Kurawa Wanda Antabbatar Dan BUZU Ne Yakai Wannan Samame. Kuma Shine Ke Addabar Ƙasar Gobir Da Gabaschin Isa.

TURJI Ya Assasa, Tareda Ƙarfafa Waɗannan Dabobin Ƴan Bindiga Na Ɗan Bokkolo Da Buzu Ta Gefen Hagunshi Da Damanshine Domin Suzama Ƙaraurawa Agareshi Na Dukan Abunda Zai Tunkaro Mazamninshi Dake Chikin Dajin FAKAI Wanda Wata Wutsiyar Dajin RUGU Ne Dake Chikin Jahar Katsina.

Tabbas Babu Abunda Mutanen Jibiya, Zurmi, Moriki, Shinkafi, Isa, Sabon Birnin,Goron,Raɓa, Da Wurno Kesonji Irin Mutuwar Turji. Domin Ya Addabi Mutanen Waɗannan Yankuna Sosai Kuma Yanada Ƙarfi, Ya tara Miyagun Makamai. Yanada Manyan Kwamandodi Aƙalla Biyar Kuma Yanada Ƴan Bindiga Aƙalla Ɗari Ukku Aƙarƙashin Kulawarshi.

Daga Ƙarshe Adalilin wannan Ɗaukewar Layin Sadarwa Da Irin Matakan Dantse Wuraren Ƴan Ta’adda Na Hanamasu Zirga Zirga. Muna Fatan Allah yasau Sumatsu Sufito Fili Domin Adamƙesu.

Allah ya kawo mana Ƙarshen Wannan Hatsabibin Ɗan Bindiga Bello Turji.

Mun ciro wannan rubutun daga shafin face Fateema Zarau page. Bayan mun tabbatar da sahihancin abin da ta rubuta

KATSINA CITY NEWShttps://www.katsinacitynews.com
Danjuma Katsina, Dan Jarida, Manazarci, Marubuci, Mamallakin Jaridun KATSINA CITY NEWS, JARIDAR TASKAR LABARAI, THE LINKS NEWS, a karkashin Kamfanin MATASA MEDIA LINKS NIGERIAN LTD

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Must Read

French Ambassador meets Zulum, to partner on Agriculture, Education

The French Ambassador to Nigeria, Ambassador Emmanuelle Bultmann said her country plans to partner with Borno State on development of agriculture, education, and the...

Commissioning ceremony of the Central Bank of Nigeria / Rice Farmers Association of Nigeria (RIFAN)

On Tuesday, January 18, 2022, I presided over the official commissioning ceremony of the Central Bank of Nigeria / Rice Farmers Association of Nigeria...

In na ci zabe, WAEC za ta zama kyauta a Najeriya- Tinubu

Asiwaju Bola Ahmad Tinubu, mai neman takarar shugabancin kasa a jami’iyyar APC ya ce idan ya zama shugaban kasa, WAEC za ta zama kyauta...

Plenary proceedings of the House of Representatives for Wednesday, January 19th, 2022

Plenary proceedings of the House of Representatives for Wednesday, January 19th, 2022 The Speaker of the House, Rep. Femi Gbajabiamila presiding. After leading the opening prayer...

You’re Not Updated, PVCs Don’t expire, INEC Tells Tinubu

The Independent National Electoral Commission (INEC) has urged Nigerians to disregard claims by a chieftain of All Progressives Congress (APC) Ahmed Bola Tinubu that...