Advert
Home Sashen Hausa Babu Abin Da Ke Tafiya Dai-Dai A Mulkin Buhari – Dr Bugaje

Babu Abin Da Ke Tafiya Dai-Dai A Mulkin Buhari – Dr Bugaje

Babu Abin Da Ke Tafiya Dai-Dai A Mulkin Buhari – Dr Bugaje

An tabbatar da cewar babu wani abu guda da ke tafiya dai-dai a mulkin Buhari, an samu mummunan koma baya abubuwa sun rincaɓe ba a san ranar samun daidaito.

Bayanin hakan ya fito ne daga bakin fitaccen ɗan siyasa shugaban kungiyar rajin kishin Arewa Dakta Usman Bugaje a yayin wata tattaunawa da gidan Talabijin da Rediyo na Liberty Abuja ya yi dashi cikin shirin Haɗin Kan Ƙasa.

Dr Bugaje wanda ya bada misali da yadda harkar tsaro ta taɓarɓare a Najeriya zubar da jinin jama’a ya zama tamkar zubar da ruwa, ya zamana babu ranar da ba’a kisan jama’a a ƙasar musanman yankin Arewacin Kasar.

“Satar jama’a da yin garkuwa da su ya zama jiki a tsakanin jama’a, mafi munin labari shine satar ɗaruruwan yara da ‘yan bindiga suka yi a ƙaramar Hukumar ƙanƙara ta jihar Katsina, a daidai lokacin da Shugaban Kasa ya ke Jihar.

Dr Bugaje ya cigaba da cewar amma abin mamaki Buhari ya gaza tashi ya je ya jajantawa iyayen yaran, ya lanƙwashe a gida ya tura wakilci wannan abin takaici ne, haka a lokacin da Boko Haram suka yi kisan gilla ga manoma a Zabarmari ta jihar Borno, Buhari bai je ba sai kawai ya tura wakilci wannan alama ce dake nuna bai san tsarin shugabanci ba, domin babu wani Shugaba a duniya da zai zamana a yi wa jama’ar shi kisan gilla amma ya kasa tashi ya je ya ganewa idonshi da jajantawa iyalan su, sai Buhari kawai.

“Ba mu san matsayin da yake akai ba, wata ɗagawa ce ko kuwa hali ne na ko in kula” ya sanya ƙafa ya yi fatali da ƙima da mutuncin jama’a.

Buhari ba ya jin shawara, dukkanin masu fada a ji a kasar nan sun yi kira a gareshi akan ya yi gaggawar sallamar shugabannin tsaro amma ya ƙi, Mutane irin su Sarkin Musulmi da hatta kan ta Majalisa, amma Buhari ya yi ƙememe.

Usman Bugaje ya bayyana cewar ba abu ne mai yiwuwa ba a rungume hannu ana kallon abubuwa na tafiya ba yadda suka kamata, matukar tura ta kai bango babu shakka al’umma zasu ɗauki mataki.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Must Read

An Naɗa Tsohon Shugaban Najeriya Goodluck Ebele Jonathan A Matsayin Shugaban Jami’ar Cavendish Ta Kasar Uganda (CUU)

An Naɗa Tsohon Shugaban Najeriya Goodluck Ebele Jonathan A Matsayin Shugaban Jami’ar Cavendish Ta Kasar Uganda (CUU) Mukamin na ‘Chancellor’ na jami’ar ta CUU ta...

“Shugaban Kasa Muhammadu Buhari Zai Gana da Dukkan Shuwagabannin Kananan Hukumomi a Kasar Nan”

LABARI DA DUMI-DUMIN SA! "Shugaban Kasa Muhammadu Buhari Zai Gana da Dukkan Shuwagabannin Kananan Hukumomi a Kasar Nan" Shugaban kasa Muhammadu Buhari zai sanya labule da...

Shugaba Buhari Ya Baiwa Kwamitin Rage Talauci Umurnin Gaggauta Ceto Mutane Milyan Dari Daga Talauci A Najeriya

Shugaba Buhari Ya Baiwa Kwamitin Rage Talauci Umurnin Gaggauta Ceto Mutane Milyan Dari Daga Talauci A Najeriya A ranar Talata, 22 ga watan Yuni, 2021,...

Iran Carries Out 1st Remote Surgery with Home-Made Robot

Iran Carries Out 1st Remote Surgery with Home-Made Robot I am sharing this with Friends because the Western MainStream Media (MSM) will NEVER show you...
%d bloggers like this: