Rahotanni sun bayyana cewa, babbar na’urar da ‘yan sanda ke amfani da ita wajan bin sayun ‘yan bindiga ta lalace.

Punchng ta ruwaito cewa tun a farkon shekarar nan ne dai na’utar ta lalace. Wasu majiyoyi da suka gayawa Punchng labarin sun ce, na’urar ta lalace ne saboda yanda aka kara bata Kulawar data dace.

Saboda yanda ‘yan bindigar ke amfani da wayar hannu wajan neman kudin fansa yasa masana ke cewa cikin sauki za’a iya gano inda suke.

Sai dai wasu ‘yan sanda ciki hadda Kwamishina sun gayawa Punchng cewa, na’urar da ake bibiyar wayoyin ta lalace tin watan Janairu.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here