Daga dama zuwa hagu; Malam Danjuma Katsina babban Editan Katsina City News da Suleiman Garba Kafin Soli Manajan Daraktan Zamani Media Crew a lokacin ziyarar

Malam Danjuma Katsina Shararren Danjarida ne, mamallakin Kamfanin Matasa Media Links dake Buga jaridun yanar gizo Katsina City News, Jaridar taskar labarai, The Links News,  da Mujjallar Katsina City News ya yi wannan maganar a ranar Litinin lokacin da Kamfanin Zamani Media Crew ya ziyarce shi a Ofishin su dake kofar kaura domin gabatar da Kamfani da kuma neman shawarwari da kulla alaƙa tsakanin su.

a ranar Litinin 4 ga watan Afrilu, Kamfanin karkashin jagorancin manajan Darakta Alhaji Suleiman Garba Kafin soli, sun kai ziyarar bangirma da neman kulla alaƙa da Kamfanin Matasa Media Links, masu buga Jaridun Katsina City News, Jaridar Taskar Labarai, da ta turanci The Links News.

Da yake gabar da jawabi  wajen, MD Kafin Soli, ya bayyana makasudin ziyarar inda yace “Kamfanin Matasa Media Links kune farkon Kamfanin Buga jaridu da muka fara ziyarta duba da yanda kukayi fice bama Katsina ba duka fadin Najeriya wajen bayyana labarai na gaskiya da kwarewa.” Inji kafin soli.

Kafin soli ya kara da cewa, “Muna so mu kulla alaka daku da kuma neman shawarwari duba da shi wannan kamfanin namu sabo ne, kuma muna son sanin abubuwa dayawa daga wajen ku, a matsayin ku na tsaffin hannu da kuka kwashe tsawon shekaru a cikin Aikin jarida.”

Sannan Kafin soli ya kuma roki Kamfanin na Matasa Media Links a karkashin jagorancin Shugaban Kamfanin Malam Danjuma Katsina, da ya bude kofar sa a Kamfanin Zamani Media Crew domin a koda yaushe zasu zo neman shawara da hadin guiwa domin aiki tare, a karshe MD Kafin soli ya tabbatar ma Malam Danjuma da cewa sun dauki fiye da Matasa goma sha takwas aiki a bangarori daban-daban da suka shafi gyara da tace Hoto, Editing na bidiyo hada rahoto da kula da yadashi.

Da yake maida jawabi Shugaban Kamfanin kuma Babban Editan Kamfanin Matasa Media Links, Malam Danjuma Katsina ya nuna jin dadi akan ziyarar gami da karfafa gwiwa akan aikin, Danjuma Katsina yasha alwashin taimakawa kamfanin ta fannoni daban daban, “Ina ganin shirye-shiryen ku kuma na yaba, kuma a koda yaushe kofata a bude take don neman shawara ko tambaya a kan abinda baku gane ba, kuma ina kara baku shawara da ku dunga shirya ma ma’aikatan naku, wani ƙwarya kwaryar zama ku gayyaci kwararru domin su kara faifaye maku Ilimi, saboda shi aikin jarida ilimi ne mai rai wanda yake rayuwa a koda yaushe kuma yana tafiya daidai da zamani. Don haka a koda yaushe ana ganin bakin abubuwa, don haka yanada kyau kusan bambancin, rubutun Social Media da rubutun jarida, ku kara sanin Fassarar (Transcribing) juya rubutu daga murya zuwa rubutu.” Inji Danjuma Katsina.

Danjuma Katsina yace, “Zamu ci gaba da neman ku a kan duk wani abu na ci gaba idan ya taso, sana kuma tun ranar da naga Takardar ku, na ce a gayyace ku, wani taro da mukayi na ‘yan jarida a nan HAYATT REGENCY, kuma munga kunje.”

A karshe anyi musayar Number waya domin tuntuba da neman shawara.

Wadanda suka rufama Shugaban Zamani Media Crew baya Sun hada da Daraktan Shirye-shirye, daraktan, Kasuwanci da Tallace-tallace, Daraktan Shafin yanar gizo, da sauran ma’aikatan,

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here