Babbar kotun daukaka ƙara dake kano ta bayarda belin Mahadi Shehu

Shiga ta farko a Babbar Kotun Tarayya dake Kano ( Lauyoyi, ma’aikatan kotu da ‘yanjaridu sun zazzauna. Alkali ya shigo, ya bada umurni an kira karar dake tsakanin Babban Sufeton Yansandan Nijeriya da Mahadi Shehu.

Bayan ‘yan mintoci ana jira daga karshe an shigo da wanda ake tuhuma, Mahadi Shehu wanda ke tafiya da kyar – da kyar yana dogara sandunan guragu.

Bayan ya zauna, alkali ya umurci lauyan maikara da ya gabatar da karar da yake yi wa Mahadi.

A nan, magatakardar kotu ya mike inda ya karanto caji guda 6 da ake yi masa dayaya bayan daya.

Dukkan caje-cajen da ake yi masa sun shafi zarge zargen da ya rika yi ma Gwamna Aminu Masari, Sakataren Gwamnatin Jihar Katsina da wasu jami’an gwamnati na karkatar da kudade daga asusun tsaro dake bankin UBA da na Fidelity.

Ana zargin Mahadi da yin ikirarin cewa an karkatar da kudaden ne ta hanyar bada gudunmuwa ga uwar Jamiyyar APC ta kasa, da sayen wayoyin salula na N849m da N856m don biyan alawus ga yansanda masu gadin aikin wutar lantarki na Lambar Rimi.

An tambayi Mahadi Shehu ya ji cajin da ake yi masa kuma ya fahimta ya ce eh! ya ji, ya fahimta.

Kotu ta sake tambayarsa ya aikata ko bai aikata ba, Mahadi ya ce bai aikata ko daya ba.

Daga nan kotu ta waiwayi lauya mai gabatar da kara da ya kawo shedu, in ya nemi Kotun da ba shi wata rana.

A karshe Alkalin Kotun Maishari’a A. Lewis Allagoa ya bada belin Mahadi Shehu akan kudi Naira Miliyan 10 tare da kawo wani mai tsaya masa wanda wajibi ne ya kasance mazaunin garin Kano kuma ya zama yana da wata kaddadara ta kasa a Kano.

Sai dai kuma alkalin ya ba da umurnin a wuce wa Mahadi zuwa gidan yari na kurmawa dake Kano har zuwa lokacin da ya cika sharuddan belin.

Daga nan ya daga zuwa 19/4/2021 don ci gaba da sauraren shari’ar.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here