Babbar kasuwar katsina bayan tashin Gobara;

©️Katsina City News Zaharaddeen Ishaq Abubakar

Harkoki sun fara dawowa a Babbar kasuwar katsina bayan tashin gobara da tayi sanadiyar rasa dukiya mai dinbin yawa,

Gobarar da ta kwashe tsawon awa takwas tana ci a ranar litanin da ta gaba inda ta kone sama da shaguna dubu da kayan cikinsu, a yau litinin kwana 7 da faruwar lamarin ‘yan kasuwa sun fito da dan abun da ya samu; sun fara kasawa a filin da yayi saura daga Gobarar.

A wani rahoton kuma Gwamnatin katsina ta kafa wani kwamiti na gaggawa domin tantan ce wadanda barnar gobarar ta shafa don duba lamarin su.

al’uma na ciki da wajen jihar ta katsina ‘yan siyasa, Attajirai da talakawa, sun nuna alhinin su, inda kawo yanzu suke ta zuwa kasuwar don duba irin barnar, da ba da gudun muwar da ta dace,

Dan Siyasa kuma dattijon jam’iyya APC tsohon Gwamnan lagos Bola Tinubu ya ziyarci kasuwar inda ya bada tallafin tsabar kudin naira miliyan 50, shima Sanata Ahamad Babba kaita sanata mai wakiltar yankin Daura shima ya kai tashi gudun mawar, kungiyar Gwamnonin Najeria, bisa wakilcin Gwamnan jihar Sokoto Aminu waziri Tambuwal da kuma Gwamnatin jihar ta sokoto, sun bada tallafin su domin Ragewa ‘yan kasuwar, raɗaɗin abinda ya same su.

Dafatan Allah ya kiyaye gaba Allah ya maida sabon Arziki.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here