Gwamnan Jihar Kano Dr Abdullahi Umar Ganduje ya bayyana cewa jam’iyyar APC zata kara bunkasa bayan kammala babban taron ta na kasa, wanda za a gudanar a gobe Asabar a Abuja.

Ganduje ya bayyana hakan ne yayin wata ganawa da ya yi da manema labarai a babban birnin tarayya Abuja.

Gwamnan, wanda shi ne Shugaban Kwamitin Tsare-tsare na Babban Taron na APC, ya ce matsalolin rashin fahimta da a ke samu a jam’iyyar, musamman game da shugabancin jam’iyyar a matakin kasa, babu wani nakasu ko rarrabuwar kawuna da za’a samu bayan taron.

Yace APC ita ce jam’iyya mafi girma yanzu a Africa, kuma yana da yakinin zata sake kafa gwamnati a matakai daban-daban a Ƙasar nan a Shekara ta 2023.

“Tun lokaci da aka kafa jam’iyyar APC muna Samar da Shugabannin mu ta hanyar masalaha, Kuma Bamu taba Samun matsala ba don haka a wannan karon ma Ina baka tabbacin ba zamu Sami wata matsala ba “. Inji Ganduje.

Ganduje ya Kara da cewa Matakin yin masalaha ga yan takara da jam’iyyar ta ke yi shi ne yake kara mata girma, kuma yace matsayinsu na masu ruwa da tsaki a jam’iyyar, zasu cigaba da tattaunawa domin shawo kan Waɗanda suka ki yarda da masalaha a zaben da za a gudanar gobe.

” Matakin da shugaban kasa Muhd Buhari ya dauka na kokarin ganin anyi maslaha abun ne da ya dace Kuma hakaan zai Kara hada Kan ‘ya’yan jam’iyyar APC a kasa baki daya”. Inji Ganduje.

Al’umma da yawa dai Suna ganin jam’iyyar APC zata iya shiga rudani bayan babban tsaron ta na kasa, Saboda yadda aka kasa Samun maslaha a tsakanin yan takarar Shugabancin jam’iyyar.

~Daily Nigerian

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here