Babban taron APC: Wani masoyin APC ya mutu a lokacin taron jam’iyyar
Labarun Hausa
Wani mai goyon bayan jam’iyya mai mulki wato All Progressive Congress (APC) ya faɗi sannan ya mutu a lokacin babban taron jam’iyyar ranar Asabar. Jaridar Daily Trustta rahoto
Ya mutu yana kan hanyar zuwa wurin taron
Magoyin bayan jam’iyyar ta APC yana kan hanyar zuwa dandalin Eagle Square, wurin da ake gudanar da babban taron, lokacin da ya faɗi ya mutu har lahira.
Wani daga cikin mutanen da ke kusa da shi ya bayyana cewa da farko yayi ƙorafin idon sa na ɗaukewa sannan ya faɗi daga baya.
Masoyan APC sun yi ƙoƙarin taimaka masa
Wakilin jaridar Daily Trust a wurin ya ga lokacin da mutane da dama magoya bayan jam’iyyar ta APC su kayi ƙoƙarin taimaka masa, sai dai hakan bai yiwu ba inda ya ce ga garin ku nan.
Wasu mutane bisa jagoranci jami’an tsaro sun lulluɓe mamacin sannan su ka tafi da shi.