Shugaban Kwamitin Riƙo na Jam’iyyar APC na ƙasa, Gwamna Mai Mala Buni ya bayyana cewa ya amince da matakan da Gwamna Abubakar Bello na Jihar Naija ya dauka a matsayin shugaban riko na wucin-gadi na kwamitin.

Buni ya baiyana amincewar ta sa ne a wata sanarwa a yau Alhamis a Abuja, yayin da yake mayar da martani ga rahotannin kafafen yada labarai na cewa ya dakatar da wasu daga cikin tsare-tsaren da Sani Bello ya gudanar.

“muna sanar da duk masu ruwa da tsaki da ‘yan jam’iyyar cewa batun dakatar da wasu ayyuka da Abubakar Sani Bello ya fara da aiwatarwa a karkashin shugaban riko kuma Gwamnan Naija, Muhammed Bello ba gaskiya ba ne.

“Don haka, duk ayyukan da aka yi a lokacin da ba na nan na amince da su kuma sun kasance masu inganci.

“Ina shawartar dukkan masu ruwa da tsaki na jam’iyyar da ‘ya’yan jam’iyyar da su yi watsi da maganar yin watsi da ayyukan kwamitin a karkashin jagorancin shugaban riko,” inji Buni.

Ya ce ya mika ragamar shugabancin kwamitin ga gwamnan Naija kafin ya tafi kasar waje neman lafiya.

Ya bukaci goyon bayan ‘ya’yan jam’iyyar don ciyar da ita gaba har lokacin babban taron jam’iyyar na kasa Wanda za’a yi a ranar 26 ga Maris.

Ana sa ran za a zabi sabbin shugabannin jam’iyyar na kasa a babban taron jam’iyyar don gudanar da al’amuran jam’iyyar.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here