Advert
Home Sashen Hausa Babban Sufeton 'yan sandan Najeriya ya bayar da umarnin kama Rahama Sadau

Babban Sufeton ‘yan sandan Najeriya ya bayar da umarnin kama Rahama Sadau

 

Babban Sufeton ‘yan sandan Najeriya ya bayar da umarnin kama Rahama Sadau

..

Rundunar ‘yan sandan Najeriya, ta bayar da umarnin kamawa da bincikar fitacciyar ‘yar fim ɗin nan Rahama Sadau, bayan wani ya kai ƙarar ta ga ‘yan sandan kan wasu hotuna da ta wallafa da suka jawo ɓatanci ga Annabi Muhammad (SAW).

Sai dai a bayanan da BBC ta samu, ‘yan sandan ba su samu nasarar kama Rahamar ba saɓannin yadda wasu kafafen yaɗa labarai suka ruwaito, amma majiya mai ƙarfi ta nuna cewa tana ƙoƙarin haɗa tawagar lauyoyinta da za ta je da su ofishin ‘yan sandan domin kai kanta.

Babban Sufeton ‘yan sandan Najeriya Mohammed Adamu ne ya bayar da umarnin kamar Rahamar bayan wani mai rajin kare haƙƙin ɗan’adam mai suna Alhaji Lawal Mohammed Gusau ya aika wa babban sufeton da wasiƙa bisa cewa Rahamar ta aikata saɓo ga annabi.

A takardar koken da Alhaji Lawal ya aika wa babban sufeton, ya shaida wa babban sufeton cewa abin da Rahama ta aikata zai iya jawo rikici domin kuwa tuni wasu malamai da matasa suka fara barazanar ɗaukar mataki, a cewarsa.

Ya kuma yi wa babban sufeton matashiya kan abin da ya faru a Kano a ‘yan kwanakin nan da kuma a Faransa wanda ya ce dama tuni al’ummar Musulmi abin ya kai su bango.

..

Ya kuma buƙaci babban sufeton ya yi la’akari da cewa bai kamata Najeriya ta ƙara tsunduma cikin wani rikici ba a daidai lokacin da take ƙoƙarin farfaɗowa daga tarzomar da ENDSARS ta jawo.

Da alama babban sufeton ya samu wannan wasiƙa ta Alhaji Lawal cikin hanzari, kuma ba tare da ɓata lokaci ba ya bayar da umarni ga kwamishinan ‘yan sanda na Jihar Kaduna domin gaggauta ɗaukar mataki don tabbatar da cewa wannan lamari bai haifar da wani abu na rashin tsaro da tada hankalin jama’a ba, kamar yadda takardar da Babban Jami’in Ofishin Sufeto-Janar mai suna DCP Idowu Owohunwa ya rattaɓa wa hannu ta nuna.

...

Mun yi ƙoƙarin jin ta bakin Alhaji Lawal Gusau, wanda ya kai Rahama ƙara domin jin ƙarin bayani, amma bai ɗaga waya baya.

Sai dai Mujallar Fim ta ruwaito cewa Alhaji Lawal Gusau ɗin sananne ne wajen shiga al’amuran da suka shafi harkar fina- finan Hausa, domin kuwa, ko a kwanakin baya sai da ya kai ƙara a kan bidiyon tsiraici wanda ake zargi na Maryam Booth ne da aka yi ta yaɗa shi a kafafen sada zumunta a kwanakin baya.

A cikin makon nan ne dai Rahama Sadau ɗin ta wallafa wasu hotuna waɗanda suka nuna surar jikinta, wanda hakan ya jawo wani ya yi maganar ɓatanci game da Manzon Allah (SAW) a ƙasan hotunanta da ta saka.

Sai dai daga baya jarumar ta fito ta ce sam ba da yawunta aka yi waɗannan kalaman ɓatancin ba, inda har ta yi bidiyo tana kuka tana roƙon gafarar Musulmai da waɗanda abin ya ɓata wa rai.

Tun kafin ta nemi gafarar, abokan sana’arta da dama na Kannywood sun fito sun yi mata raddi mai zafi, haka ma wasu sanannun mutane a kafafen sada zumuntar sun yi mata raddi da jan kunnenta.

Kauce wa Twitter, 1

Karshen labarin da aka sa a Twitter, 1

Sai dai bayan haƙurin da ta bayar da kuma nadamar da ta yi, wasu sun sassauta kalamansu kanta da ba ta shawarar kada hakan ya sake faruwa, wasu kuma na nan a kan bakarsu na cewa ba za su yafe mata ba.

KATSINA CITY NEWShttps://www.katsinacitynews.com
Danjuma Katsina, Dan Jarida, Manazarci, Marubuci, Mamallakin Jaridun KATSINA CITY NEWS, JARIDAR TASKAR LABARAI, THE LINKS NEWS, a karkashin Kamfanin MATASA MEDIA LINKS NIGERIAN LTD

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Must Read

NIMET Installs Message Dissemination Platforms At Abuja, Kaduna, P/H Airports #Positivefacts

https://www.facebook.com/101788642037662/posts/pfbid02SkXT7vgAdTkuHz5gW6EaSFt3qZoc4hVMtBMXRMw6SzFv1da5ujPAsEmWyd535tYgl/ Nigerian Meteorological Agency (NiMET) has procured and installed seven automatic message dissemination platforms at Abuja, Kano, Lagos, Maiduguri, Kaduna, Enugu, and Port Harcourt airports. The...

FISHERIES PROJECT CREATES JOBS TO OVER TEN MILLION NIGERIAN #PositivefactsNG

https://www.facebook.com/101788642037662/posts/pfbid0Gc6v3B4e1KT8u7qGbmcMUofbzSaejnB1PTcdjHrBSUaUtQA28bQNeQ3qgLAnhBfzl/The federal government under the leadership of president Muhammadu Buhari, GCFR, has create over ten million jobs to Nigerian through fisheries project, the honourable minister...

Muna kira ga Gwamnati ta taimaka mana kada ruwan damuna ya share mana gidaje….. Mutanen Unguwar Ɗoroyi a cikin garin Katsina.

Muna kira ga Gwamnati ta taimaka mana kada ruwan damuna ya share mana gidaje..... Mutanen Unguwar Ɗoroyi a cikin garin Katsina. Zaharaddeen Ishaq Abubakar @Katsina...

Yunƙurin Ficewar Sanatoci 20 Daga APC: Ku Nemawa Kanku Mafita Tun Kafin Wuri Ya Kure Maku – Hon. Ɗanlami Kurfi

Kamar yadda rahotanni ke cewa akwai kusan Sanatoci 20 na jam'iyyar APC da ke kokarin ficewa daga jam'iyyar saboda wasu dalilai da suka ƙi...

MATSALAR TSARO: Yanda Al’umar garin Mada, dake ƙaramar Hukumar mulkin Gusau suke barin gidajen su…

Matsalar Tsaro: Yadda al'umar garin Mada dake karamar hukumar mulkin Gusau ta jihar Zamfara ke barin matsugunnansu a safiyar yau Asabar sakamakon ta'azarar hare-haren...
%d bloggers like this: