Babban Burina A Kullum Shine Naga Nasa Al’umma Farin Ciki, Cewar Hon Alh Ado Iris (ADO RODI )

Daga Muhsin Tasi’u Ya’u

Tattaunawa da gwarzon dan gwagwarmaya matashi abin koyi Hon Alh Ado Iris (ADO RODI )
Tarihin Rayuwarka
An haife ni a 1982 a unguwar sheka, na taso nayi shekaru Uku ko hudu tare da mahaifina kuma dan kasuwa ne, ya kaini makarantar allo ni da yayana, mun zauna a makarantar allo har kusan shekaru 30 zuwa 35 sakamakon bamu dade ba mahaifinmu Allah yayi masa rasuwa, ban samu nayi makarantar boko da wuri ba sai bayan wasu shekaru sannan na shiga makarantar yaki da jahilci inda nayi firaimare da sakandare duk a shekaru 7 kuma na zamo mai kwazo duba da karatun Al’qurani da Allah ya bani a makarantar ‘Abacha Youths Center’, har ya kasance wanda suke makarantar gwamnati suna zuwa muna koya masu karatu sannan bayan na gama saina daura inda na samu kwalin NCE.
Fara Kasuwancinka
To Alhamdulillahi domin kasuwanci daman gadar sa mukayi a gurin mahaifinmu, mahaifina dan kasuwa ne a kofar nasarawa shagunan su ne wannan Wanda aka ture su lokacin buhari sabo da haka mahaifina dan kasuwa ne kuma nima sai na tashi da son kasuwanci na zama dan kasuwa sai na kasance bani da kasala bani da rashin jure kasala ko mutuwar zuciya tun ina tafiya ina yin kara ma’ana itace na girki wanda zan kawo cikin gari na siyar na samu abunda zan rufawa kaina asiri na bukatuna, har nazo na fara zuwa kasuwar yan lemo na dinga tsinto lemo nazo unguwar mu ina siyarwa daga nan kuma sai muka juya dauko irin su yalo da gyada da albasa da dai sauransu, bayan mun gama wannan sai muka Koma kamfani a lokacin an bude kamfanin dangote na flour inda mukayi dako a ciki, mun samu kamar shekara uku muna wannan gwagwarmaya daga nan muka Koma kasuwa inda nan ma mukayi dako sabo da muna hazaka bamu dade ba kawai sai mukayi shawara mu fara sana’a inda muka fara da abunda ake cewa kayi na yi, har ta kai da wani yayan mu yana mana fada gudun kada mu dauko abun da yafi karfin mu muka jure har in munga kwastoma sai mu dunga rugawa a guje don saurin taran sa, daga nan na fara zama dan kasuwa har na fara da samun naira dubu goma (N10,000), akwai wani mai gidana wanda nake saran kaya a wajansa, bayan naga na samu dubu goman farko sai na fara tunanin ya zanyi na kara samun wata dubu goman don na ingata kasuwanci na na raba gomar farko na ajiye ta a waccan sana’ar wannan dana kara samu na rike a aljihu na ina Juya su suma daban.
Tarihin Siyasarka
Farkon ubangida na da nafara ta dalilin sa Alhaji Jafaru Dan Maliki bayan na dan jingine kasuwanci muka fara harkar siyasa gadan gadan aje nan aje chan kuma a kafa nake wannan yawon siyasar ina tashi daga dan maliki naje panshekara a kafa na dawo na tafi na’ibawa a kafa da wasu wajajen da yawa duk a kafa, ana cikin haka dai sai aki sabom chairman Sagir Panshekara a karamar hukumar Kumbotso inda har ya kasance ina da albashi duk wata ana bani naira dubu hudu (N4000) kuma ni wannan dubu hudun kamar kallon dubu dari N1000 nake mata a lokacin kuma a hakan tana kashe mun ‘yan bukatuna na karshen wata daga baya sai na bar gidan sagir panshekara na koma gidan wani daban inda kuma cikin hukuncin Ubangiji a shekara ta 2007 sai muka fadi zabe manniru babba yaci wanda shine yanzu dan majalisa mai wakiltar Kumbotso Local Government a majalisar tarayya da naga haka sai nace tunda mun fadi ya kamata na koma kasuwa tunda Ahamdullilah ina da nasibi a kasuwa. Bana mantawa naje wajan wani kwamishina akan ya taimake ni da dubu hamsin na fara kasuwanci sai yace bai san irin gudummuwar da nake bayarwa ba a karamar hukumar Kumbotso don haka sai ya tura ni wajan jagororin mu na wannan lokacin sai ya kasance wanda aka tura ni wajan su domin su wakilce ni suje su fada masa wacce irin gudummawa nake badawa a Kumbotso sai ya kasance su wannan mutanen suka dunga kwan-gaba kwan-baya suma kaini wajan sa ma sunki wannan kudin a karshen dai ban same shi ba bana mantawa ranar karshen muna gidan shi Nasiru Zico har ma muka samu sabani sabo da bai kaini wajan shi kwamishina ba mukayi cacar baki da shi a cikin mutane bana mantawa a waje muna waje ya kira wasu wanda muke tare a waje su shiga gidan sa suyi kalaci bayan sun shiga aka basu shayi da madara da kwai ni kuwa ko karyawa banyi ba nazo gidan sa, a karshe ina kofar gidan sa bayan sun gama sai Aminu mai dawa ya fito ya tambaye ni ina zanje don ya rage mun hanya akan vespa sai ya rage mun ya kaini kasuwar Sabon gari ya ajje ni a dai dai kwanar da zan Shiga layin mu, cikin hukuncin ubangiji daga wannan lokacin sai ya kasance a ban fito da kudi ba a kullum sai na fito da naira dubu tamanin ta wannan lokacin cikin hukuncin ubangiji a kuma a cikin dan takaitaccen lokacin Allah ya fara bani wannan nasarar na samun wannan kudin wanda a mako ranar lahadi ne kawai bana samu, a cikin hukuncin Allah Komai ya warware mun da bani da gida na samu na gina gida a cikin nan unguwar mu muna zaune a haka bayan Allah ya bani kusan yara guda Uku sai gidan yai mana kadan, sai na fara proposal nazo na sai fili a bakin titi inda nasai fili babba na gina, abinda yasa mun kaimi a shi wannan tsohon gidan ya kasance bandaki guda daya ne, kana cikin bandaki sai kaji yaro ya saka maka kuka a bakin kofar bandakin shi yasa na sai wannan filin a bakin titi kuma cikin kankanin lokaci wanda bai wuce wata takwas ba na gama wannan ginin a nan bakin titin unguwar tamu, har ta kai ga mutane wasu suna cewa wiki nane wasu na cewa bazai yiwu ba ba nawa bane sabo da ai suma a cikin kasuwar suke mai yasa su basiyi ba sai ni hakan bai hanani toshe kunne na ba naci gaba da aiki na gadan-gadan na gama na tare haka kuma a cikin gidn sai da nayi bandaki guda takwas ga dakuna wani dakin ma sai ayi shekara ba a bude ba, a wannan lokacin na mallaki rumfa na zama cikakken dan kasuwa kuma akwai yara da suke zaune a karkashi na kuma sana’ar da nake yi itace duk wani abu wanda ya shafi buhu kuma har gobe Ita nake.
Mai Yabaka Sha’awa Ka Fara Siyasa
Ni mutum ne mai son ya taimaki Al’umma sai naga Yadda yan siyasa suke taimakon mutane a wannan lokacin wannan shi ya bani sha’awa na dage sai nayi siyasa domin ina so nasa Al’umma Farin Ciki a rayuwata.
Ya Kake Hada Kasuwanci Da Siyasa
Ba zai bada wani wahala sosai ba ko yau kafin kazo naje kamfanunnuwan da nake mu’amala dasu na dauki kaya na tura kasuwa sannan na fito nan wajan siyisa nan cikin office dinnan.
Wane Kira Zakayi Kan Matasa Kada Su Rungumi Siyasa Ita Kadai Ba Tare Da Sun Hada Da Sana’a Ba
Ina Shawartar yan uwa na matasa kar Ku zama sai dai a Baku, Ku zama masu bayarwa saboda Indai zaka dogara da wannan baza ka samu abunda kake so a rayuwa ba domin shi kasuwanci Komai kankantar sa yana bawa kowa tsoro a duniya Indai kana karamin dan kasuwa ci gaba da abun da kake yi ka dan samu wani abu sai ka shigo harkar siyasa ko kuma ka kasance kada kace da Ita zaka dogara ko dan mutuncin ka, ba wai ana hango kana a fara tsaki ana gashi can zaizo ya roke ni, ina kira ga matasa da suyi koyi da Hon Hasan Garba Farawa saboda akwai wanda yayi min Nisan da wahala na kamoshi muttum ne wanda duk abinda zaiyi da dakiyar sa yake ba wai sai ya jira an turo masa kudi ba ina addua Allah ya taimake shi.
Wane Abu Ne Na Farin Ciki Da Ya Taba Faruwa Da Kai Wanda Baza Ka Manta Ba A siyasa
Alhadulillah abun farin ciki da ya taba faruwa da ni akan bawa Hassan Garba award a karkashin kungiyata Kumbotso sabuwa, a lokacin ya yabe ni sosai cikin dubban jama’a sannan gobe ‘yan wannan kungiya su dawo akwai nadin super V Councillor Na Community nasan ni za’a bawa mutane ma haka wannan abun sai da yasani kwalla kuma ba wai wani abu bane wannan office din da aka bani ba wai wani abu son samu a cikin sa ba sabo da Sana’a ta da nake yi Yana kawo mun fiye da abun da zan samu a asu rangwamen gata A yanzu na samawa kuma sama da mutum arba’in aiki arumfata akwai sama da mutum sha biyar wanda a karkashina suke ina da dan karamin kamfani wanda shima akwai kusan mutum bakwai ko guda zan gina to sai na fitarwa da yan unguwar kwalbatu sannan na zuba kasa kuma duk wannan abubawan da na fada ba da kudin local government nake ba da kudi na nake har ta mar duk abunda kunya ta kumbitso sabuwa a karkashin wannan kungiya kamar masu karayar cinya wani dubu dari wani dubu hamsin da sauransu to ni irin wannan abubuwan suna dadamun rai sosai.
Kiranka Na Karshen
To ni kirana ga matasa shine har kullum duk wanda Baka so ba bakin ciki zakai masa ba, in ka nayi masa bakin ciki to lallai dagawa sama zaiyi. Akwai wayanda basa san alheri in suka ga ana alheri hankalinsu tashi yake domin in nace zakai haka kamar Baka yarda Da Allah ba.
mohseeyn10@gamail.com/0806485331

 

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here