Babban Alkalin Alkalan Kotunan Birnin Tarayya, Abuja Ya Ajiye Aiki

Rahotanni daga birnin tarayya Abuja na bayyana cewar Sabon babban alkalin kotun birnin tarayya Abuja, Justice Salisu Garba ya yi murabus da kanshi bayan an nadashi a matsayin mai gudanarwa na NJI.

An samu wannan sanarwar ne a wata takarda wacce hadimin CJN na fannin yada labarai, Ahuraka Isah ya gabatar a ranar Litinin ga manema labarai dake babban birnin kasar.

A cewarsa, NJIBG, Karkashin shugabancin babban alkalin Najeriya, CJN, Justice Tanko Muhammad, ta amince da nadin Garba.

Justice Garba, wanda shine babban alkalin Birnin tarayya Abuja har zuwa lokacin da yayi murabus zai cigaba da aiki a NJI.

An rantsar dashi a matsayinsa na babban alkalin FCT a ranar 7 ga watan Yuni kuma ya kamata yayi murabus ne a ranar 10 ga watan Oktoba lokacin da zai cika shekaru 65.

An haifi Garba ne a ranar 10 ga watan Oktoban 1956 a karamar hukumar Malumfashi dake jihar Katsina, kuma an rantsar dashi a matsayin lauya a 1984 kuma ya kammala bautar kasarsa a 1985.

Ya cigaba da aikinsa a matsayin lauya na tsawon shekaru 3 bayan bautar kasarsa. An nada shi a matsayin alkalin kotun majistare dake Abuja a 1989 sannan ya yi aiki a matsayin rijistira a babbar kotu dake Abuja a 1998.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here