Home Sashen Hausa BA'A SAMU DOREWAR CIGABA, BA TARE DA AIWATAR DA WADATATTUN MANYAN AIYUKA...

BA’A SAMU DOREWAR CIGABA, BA TARE DA AIWATAR DA WADATATTUN MANYAN AIYUKA , INJI SHUGABA BUHARI, A YAYIN DAYA GANA DA WAKILIN KASAR CHINA.

BA’A SAMU DOREWAR CIGABA, BA TARE DA AIWATAR DA WADATATTUN MANYAN AIYUKA , INJI SHUGABA BUHARI, A YAYIN DAYA GANA DA WAKILIN KASAR CHINA.

Fassara: Hon. Buhari Sallau Hadimin Shugaban kasa Muhammadu Buhari Bangaren Rediyo da Talabijin.

Shugaba Muhammaadu Buhari yace, Dorewar samun Cigaba ba mai samuwa bane, da zarar kasa tanada gibi gurin samun kayakin aiki,

Shugaban yayi wannan Magana ne ranar Talata a fadar Gwamnati dake Abuja, a yayin daya karbi Mista Wang Yi Wakili kuma Ministan Harkokin wajan Jamhoriyar Al’ummar kasar China.

“Mun godewa kasar China bisa Mara mana baya a fannoni Daban daban; gurin Gina Hanyoyin Jiragen Kasa, Hanyoyin Moto, Lantarki, Tsaro, da sauran Hanyoyi da dama. Kuna taimakon mu don rage gagarumin Gibi da muke dashi a manyan aiyuka, Muna Farin ciki da Haka.

Baza’a taba samun Dorewar cigaba ba, batare da samun Cigaba a fannin aiwatar da manyan aiyuka. Inji Shugaba Buhari.

Shugaban yayi Alkawari cewa Kasar Najeriya zata cigaba da mutunta abinda ya wajabta a fannin Dangantaka tsakanin Jamhoriyar Al’umman kasar China, “a dai dai Sa’ilin da kasar ke aiwatar da manyan abubuwa daban daban, wanda muna farin ciki dashi matukan gaske.”

Mista Wang Yi ya yaba kan abinda yakira “Amintaka na kut da kut da Abokantaka” tsakanin Shugaba Buhari da Takwarar sa Xi Jinping na kasar China, ya lura cewa hakan “Yayi sanadiyar yin Yarjeniyoyi tsakanin kasashen biyu.”

Ya kara da cewa kasar China tana Son fara aiwatar da aiyukan Difulomasiyyar ta na wannan Shekara a Afirka, Shine ta zabo Najeriya a matsayin kasa ta fari a shekarar 2021, tunda a wanann Shekarar ce kasashen biyu zasu cika Shekaru Hamsin 50 da kulla Dangantakar Diplomasiyya.

Wakilin na kasar China ya bayyana Najeriya a matsayin kasa babba dake da tagomashi a Nahiyar da Kasashen Duniya, ya kara da cewa: “Mun Aminta, da Fahimtar mara baya ga juna. Zamu chigaba da Daraja Juna.”

Mista Yi, yace kasar sa zata karfafa gwiwar Kamfanonin kasar China dasu kara zuba jari a Najeriya, yayin kuma da ita kasar ta China zata so cigaba da musanya fasahohi da Dabaru da Najeriya a fannoni irin su Fasahar Kasuwancin na zamani, Tsaro, da Sauran su.

Femi Adesina:
Mashawar ci Na Musamman ga Shugaban Kasa a Fannin Yada Labaru da Wayar da kan Jama’a.
05 ga watan Janeru 2021.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Must Read

Salihu Tanko Yakasai na hannunmu – DSS

Salihu Tanko Yakasai na hannunmu - DSS Rundunar 'yan sandan farin kaya ta DSS ta tabbatar da kama Salihu Tanko Yakasai, tsohon mai taimaka wa...

Ansako ɗaliban makarantar Kagara da aka sace

GSC Kagara: An sako mutum 41 da aka sace a makarantar Kagara ta Jihar Neja An sako ɗaliban makarantar Kagara da malamansu da ma'aikata guda...

PRESS RELEASE ; GANDUJE SACKS MEDIA AIDE

PRESS RELEASE GANDUJE SACKS MEDIA AIDE Governor Abdullahi Umar Ganduje of Kano state has relieved his Special Adviser on Media, Salihu Tanko Yakasai of his appointment...

KANO STATE POLICE COMMAND DIARY 26/02/2021

KANO STATE POLICE COMMAND DIARY 26/02/2021 7 DAYS ACHIEVEMENTS OF CP SAMA'ILA SHU'AIBU DIKKO, fsi IN KANO STATE ... As 9 Kidnapping Suspects, 8 Armed Robbery...

Bamu da Adalci, Dole ne mu cire batun Siyasa idan ba Haka ba Muna gidajenmu zamu Hallaka ~Inji Atiku Abubakar..

Bamu da Adalci, Dole ne mu cire batun Siyasa idan ba Haka ba Muna gidajenmu zamu Hallaka ~Inji Atiku Abubakar.. Tsohon mataimakin Shugaban Kasa Atiku...
%d bloggers like this: