Advert
Home Sashen Hausa Ba Zan Bari a Tada Zaune Tsaye Ba, Gwamna Filato Ya Yi...

Ba Zan Bari a Tada Zaune Tsaye Ba, Gwamna Filato Ya Yi Kakkausan Magana Bayan Kashe Musulmai a Jos

Daga Yahya Abdullahi Birnin Gwari

– Gwamnan jihar Filato, Simon Lalong, yace sam ba zai lamurci duk wani yunkuri na tada zaune tsaye a jiharsa ba

– Gwamnan ya faɗi haka ne bayan ya kai ziyarar duba wasu daga cikin waɗanda lamarin Jos ya shafa

– Lalong yace lokaci ya yi da zai sa kafar wando ɗaya da duk wani dake kokarin dawo da hannun agogo baya a jiharsa

Gwamnan jihar Filato, Simon Lalong, yace ba zai lamunci duk wani yunkuri na tada rikici a jiharsa ba ta hanyar yaɗa labaran ƙarya, kamar yadda the cable ta ruwaito.

Aƙalla matafiya 22 aka kashe a wani hari da aka kai kan hanyar Rukuba, karamar hukumar Jos ta rewa, jihar Filato.

Harin, wanda aka kaiwa wasu jerin motocin Bas dake ɗauke da mabiya addinin musulunci dake kan hanyarsu ta komowa Ondo bayan halartar wa’azi a Bauchi, ya bar wasu mutum 14 cikin rauni.

Da yake jawabi bayan ziyarar da yakai wa wasu daga cikin waɗanda lamarin ya shafa, Lalong yace gwamnati zata cafke tare da hukunta kowaye ta samu da yaɗa labaran karya da ka iya tada wutar rikici.

Gwamna Lalong yace:

“Ba zamu bari a tada rikicin addinai ba, mutane su dakatar da yaɗa labaran da basu da asali, irin wannan kisan na faruwa ne ta sanadiyyar haka.”

“Ina tabbatar muku zamu sa kafar wando ɗaya da mutanen dake yaɗa sakonnin karya waɗanda ke jawo ana hallaka mutanen da ba su ji ba basu gani ba.”

“Wannan gargaɗi ne kai tsaye ga duk wanda keson dawo mana da abinda muka mance da shi. Lokaci ya yi da zamu ɗauki mataki kan waɗannan mutanen duk mukaminsu.”

Gwamnan ya kara da cewa ya kai wannan ziyarar ne domin duba yadda mutane ke ɗa’a ga dokar zaman gida da gwamnatinsa ta sa a yankin.

Zuwa yanzun rundunar sojin Operation Safe Haven ta kame mutum 12 da ake zargin suna da hannu a kisan.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Must Read

Shugaba Buhari ya nemi kasashen duniya su yafewa Najeriya bashin da suke binta

A yayin da yake gabatar da jawabi a zauren majalisar dinkin duniya a ranar Juma'a. Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya nemi manyan kasashen duniya...

Bangaren aikin jarida na H.U.K Poly sun yaye kwararrin ‘yan social media a Katsina

Bangaren aikin jarida na H.U.K Poly sun yaye kwararrin ‘yan social media a Katsina Saifullahi Kuraye‎ September 24, 2021 2 min read Bangaren aikin jarida na...

Hukumar Hana Fasa ƙwabri ta ƙasa wato Custom ta ƙwato Babura Ɗari Biyu da Biyu a Jihar Katsina…

Shugaban Hukumar Ƙwastam na Jihar Katsina Mr. Chedi ne ya bayyana hakan ne a Yau Juma'a cewa tsakanin watan Agusta zuwa Satumba Hukumar ta...

Dan Najeriya ya fiye tsogwami: da ₦500 kacal sai aci a ƙoshi……Inji farfesa Segun Ajibola

Da Naira Dari Biyar ( 500 ) kacal Zaka Iyaci Ka Koshi a Najeriya, Cewar Wani Farfesa, Masanin Tattalin arziki... Tsohon shugaban kwalejin ma'aikatan bankin...

Rail project will not displace host communities-FG

Radio Nigeria The Federal Ministry of Transport and that of Environment have given assurance to residents along the proposed stretch of land demarcated for the...
%d bloggers like this: