BA ZABEN KANANAN HUKOMOMIN BANE YADACE AYI, AJIRA YANKE HUKUNCIN KOTUN ALLAH YA ISAH YAFI DACEWA AYI A KATSINA
Ra’ayin Comr. Mai-Iyali Katsina
Kimanin Kusan watanni Sittin da ukku kenan (63) Gwamnatin Katsina Karkashin Mulkin Rt. Hon. Aminu Bello Masari Gwamnan Katsina na yanzu ya tsaida zababbun Shugabannin Kananan hukomomi na jihar katsina wanda Idan baku manta ba ya tsai dasu ran 10-07- 2015 wanda a lokacin sun yi wata 09 da kwana 10, sauran su wata 14 da kwana 20 kacal cikin watannin 24 wanda doka da kuma kundin tsarin mulkin Najeriya yatana da
Wasu rahotanni sun fita akan cewa tun a wancen lokacin akwai Lauyoyi da kuma Masu shari’a da suka bama Hon. Aminu Bello Masari shawara da kada ya tsaida wadan nan Ciyamomin domin yin hakan bazai haifar da ‘Da mai ido ba, Idan da zasu bashi shawara da yai hakuri ya barsu su ida Zangon mulkin su shi yafi, Domin tsaida su sabama dokar kasa ce, Amma a lokacin baiji wannan shawara ba
Tun bayan Tsai da zababbun Ciyamomin kananan hukomomin jihar katsina Sai Jam’iyyar PDP ta jihar katsina karkashin Jagoranci Hon. Salisu Yusuf Majigiri Suka gar zaya zuwa kotu domin neman hakkin Sauke Ciyamomin ta da akai ba’a kan ka’ida ba zuwa yanzu da nike wannan magane Shari’ai taje Supreme Court (Kutun Allah ya’isa) Wanda ko wane lokaci za’a iya zaman yanke hukuncin wannan shari’a
Kirana ga Sanata Ahmed Babba Kaita na Jam’iyyar APC Sanata maiwakiltar Shiyyar Daura, Matsayi irin nashi wanda yake rike dashi yanzu Inaganin yana da dama dazai iya tuntubar sauron Sanatocin masu wakilcin Katsina ta tsakkiya da Shiyyar Funtua Domin suje sunemi Alfarma azo a yanke hukuncin shari’a Domin komi yazo karshe bawai yazo saman Facebook yana gargadin Gwamnatin katsina da kada tasake kaka bama kananan hukomomi ‘yan kwamitin riko ba