Advert
Home Sashen Hausa Ba Za Mu Zuba Ido Mu Ga Ana Cin Zarafin Yara Da...

Ba Za Mu Zuba Ido Mu Ga Ana Cin Zarafin Yara Da Sunan Bara Ba, Cewar Gwamnatin Kaduna

Ba Za Mu Zuba Ido Mu Ga Ana Cin Zarafin Yara Da Sunan Bara Ba, Cewar Gwamnatin Kaduna

Daga Tukur Sani Kwasara

A kokarin gwamnatin jihar na ci gaba da yakar cutar corona da yawon, hukumar yaki da cutar ta corona ta yi nasarar ceto yara kimanin 160 daga wuraren da suka saba doka. Yara ‘yan asalin jihohin 13 ne da suka fito daga kudu da Arewacin Nijeriya. Wasun su ma bakin haure ne daga kasashen Benin, Burkina Faso da Nijar.

Wurare da aka bankado yaran an gano sun saba dokar rufe makarantu don gudun yaduwar cutar corona da aka kafa tun a watan Dimsaba, 2020. Haka kuma dokar ta shafi yunkurin gwamnatin Kaduna na mayar da almajirai jihohin su na asali domin ci gaba da neman ilmi a gaban iyayensu.

Gwamnatin Kaduna tana mai tunatar da kungiyon masu zaman kan su, shugabannin addinai, cewa tana da dokoki da sharruda na bada damar gudanar da neman ilmin yara ga makarantun da suka yi rijista. Domin ganin su ma almjirai an kawata sha’anin karatun su kamar sauran yara masu gata.

Rahotanni sun nuna cewa tun daga watan Maris, 2020 zuwa yanzu, gwamnatin Kaduna ta kama yara almajirai kimanin dubu 31,092, inda ta mayar da su zuwa jihohin su, tun bayan da gwamnonin Arewa suka kudiri aniyar dakile cin zarafin da ake yi wa yara da sunan almajiranci. Wanda kuma tun daga wannan lokacin ne gwamnatin ta dukufa wajen zakulo irin wuraren da ake kange yara tana ceto su tana mayar da su wurin iyayensu domin ci gaba da neman ilmi a gabansu.

Biyo bayan wannan tsari, gwamnatin Kaduna ta ceto yara 1,118 daga jihar ta mayar da su jihohinsu na asali.

Haka kuma a yayin sintiri makamancin haka da hukumar da ke da alhakin ceto yaran suka fita a makon da ya gabata, sun ceto yara 160 wadanda kuma tuni aka gano jihohinsu.

Daga cikin su akwai ‘yan jihar Kebbi guda 16, Abuja 2, Kano 15, Katsina 15, Zamfara 8, Sokoto 1, Nasarawa 12, Neja 5, Kwara 4, Kogi 2, Oyo 2, Kaduna 68.

Sai kuma yara bakin haure daga kasashen Nijar (5), Burkina Faso (3) da Benin (1).

Yanzu haka an killace yaran domin duba lafiyar su game da cutar corona daga bisani kuma a mayar da su jihohin su na asali.

Gwamnatin Kaduna ta kuma yi kira ga iyayen yara da su kasance masu baiwa ‘ya’yan su duk wani hakki na tarbiyyantarwa kamar ba su ingantaccen ilmi, ciyarwa, tufatarwa, domin yin watsi da yaran ya sabawa addini da al’adunmu. Sannan kuma ya sabawa dokar kasa ta baiwa yara ilmi, dokar walwalar yara da kuma dokar tallace-tallace. Don haka dole ne hukumomin da suke da alhakin dakile matsalolin su ci gaba da aiki tukuru domin kawo karshen matsalar.

Sanarwar hakan ta fito ne daga mai taimakawa Gwamnan Kaduna kan harkokin yada labara,
Mista Muyiwa Adekeye

KATSINA CITY NEWShttps://www.katsinacitynews.com
Danjuma Katsina, Dan Jarida, Manazarci, Marubuci, Mamallakin Jaridun KATSINA CITY NEWS, JARIDAR TASKAR LABARAI, THE LINKS NEWS, a karkashin Kamfanin MATASA MEDIA LINKS NIGERIAN LTD

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Must Read

Gwamna Masari ya Jinjinama Yan mazan jiya, wajen bikin tunwa dasu a ranar Asabar

Maigirma Gwamna Aminu Bello Masari yayi jinjina ga 'yan mazan jiya da suka sadaukar da rayuwar su domin ganin wannan kasar bata wargaje ta...

AFCON 2021: Nijeriya ta lallasa Sudan 3-1

AFCON 2021: Nijeriya ta lallasa Sudan 3-1 Tawogar Ƙwallon Ƙafar Nijeriya, Super Eagles ta lallasa takwararta ta Sudan da 3-1 a gasar ƙwallon ƙafa ta...

It was mistake electing Buhari as President – NEF

Hakeem Baba-Ahmed, the Director, Publicity and Advocacy, Northern Elders Forum (NEF), has said that it was a big mistake done in the country by...

GOVERNOR AMINU BELLO MASARI ORDERS FOR THE REOPENING OF FILLING STATIONS, CATTLE MARKETS IN KATSINA STATE

PRESS RELEASE GOVERNOR AMINU BELLO MASARI ORDERS FOR THE REOPENING OF FILLING STATIONS, CATTLE MARKETS IN KATSINA STATE -------------------------------------------- His Excellency the Governor of Katsina State Rt....

2023: Tun ina matashi na fara sana’ar siyar da manja a Maiduguri, kasuwanci ba bako na bane -Uzor Kalu

Tsohon Gwamnan Jihar Abia, Sanata Uzor Kalu, ya bayyana yadda ya fara sana’a da yadda ya zama biloniya tun ma kafin a kafa PDP. A...