Ba za a yi zaɓe a Anambra ba sai an sako Nnamdi Kanu – IPOB

IPOB

Shugabannin ƙungiyar masu fafutikar kafa ƙasar Biafra a kudancin Najeriya, Indigenous People of Biafra (IPOB), ta bai wa gwamnatin Najeriya wa’adin mako ɗaya da ta saki jagoranta Nnamdi Kanu.

Sharaɗin da ƙungiyar ta bayar ya ce idan ba a saki Mista Kanu ba za ta tsayar da dukkan ayyuka cak a yankin kudu maso gabashin ƙasar daga 5 zuwa 10 ga watan Nuwamba.

Hakan na nufin ba za ta bari a gudanar da zaɓen gwamna ba a Jihar Anambra wanda hukumar zaɓe ta INEC za ta yi ranar 6 ga watan na Nuwamba.

IPOB ta yi amanna cewa ba za a yi wa Mista Kanu adalci ba a shari’ar da yake fuskanta ta cin amana da neman raba ƙasa a gaban Babbar Kotun Tarayya.

Sai dai shugaban INEC, Farfesa Mahmud Yakubu, ya ce sun shirya tsaf don gudanar da zaɓen, yana mai cewa “mun farfaɗo daga hare-haren da aka kai kan gine-ginenmu”.

‘Yan ƙungiyar ta IPOB na ci gaba da kai hare-hare a kan ‘yan siyasar yankin da ɗaiɗaikun mutane waɗanda suka ƙi bin umarnin da suka bayar na zaman gida duk ranar Litinin har sai an sako jagoran nasu.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here